Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Kai-tsaye: Wakilan Amurka, Turai da Larabawa sun yi kira a kai zuciya nesa tsakanin Isra'ila da Lebanon

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 268 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,834 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 86,858 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 0036 GMT — Masu shiga tsakani daga Amurka, Turai da...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Wakilan Amurka, Turai da Larabawa sun yi kira a kai zuciya nesa tsakanin Isra'ila da Lebanon
Em resumo

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 268 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,834 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 86,858 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 0036 GMT — Masu shiga tsakani daga Amurka, Turai da...

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 268 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,834 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 86,858 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 0036 GMT — Masu shiga tsakani daga Amurka, Turai da ƙasashen Larabawa sun ƙara ƙaimi wajen ganin an kauce wa shiga gagarumin yaƙi tsakanin Isra'ila da mayaƙan Hezbollah na ƙasar Lebanon waɗanda ke samun goyon bayan Iran, suna masu fargabar watsuwarsa zuwa sauran sassan Gabas ta Tsakiya kamar yadda aka yi hasashe watanni da dama da suka wuce. Iran da Isra'ila sun yi musayar yawu ranar Asabar sannan Iran ta ce yaƙin da za a yi zai kasance "mai matuƙar muni". Yanzu dai babu tabbas game da tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda hakan ne kawai zai sa Hezbollah da sauran ƙungiyoyi da Iran take mara wa baya su sauƙaƙa shirinsu na gwabza yaƙi da Isra'ila. Ganin cewa babu ci gaba a tattaunawar tsagaita wuta, jami'an diflomasiyya na Amurka da sauran ƙawayenta sun gargaɗi Hezbollah game da far wa Isra'ila da yaƙi.