Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 422 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,382 da jikkata fiye da mutum 105,142. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara. 2041 GMT — ƙungiyar samar da abinci ta World Central Kitchen (WCK) ta dakatar da aiki a Gaza sakamakon harin da Isra'ila ta kai ta sama kan motar dake ɗauke da ma'aikatanta, wanda ya kashe mutum biyar. A cikin wata sanarwa a X, ƙungiyar ta bayyana damuwa kan lamarin, ta kuma tabbatar da cewa har yanzu tana tattara bayanai. "Muna cikin jimamin bayyana cewa hare-haren jiragen sama a Gaza sun faɗa kan motar dake ɗauke da ma'aikatan agaji na ƙungiyar World Central Kitchen," kamar yadda sanarwar ta bayyana. 2114 GMT — Majalisar Faransa ta goyi bayan soke taro da Rima Hassan za ta gabatar Karin labarai ???? Wata sanarwa da majalisar ta fitar ta ce tana la'akari da ɗaukaka ƙara dangane da ƙalubalantar soke jawabin da aka shirya gudanarwa a jami'ar Sciences Po University. Majalisar ta yanke hukuncin cewa soke taron da hukumomin makarantar suka yi bai wani take haƙƙin faɗin albarkacin baki na a-zo-a-gani ba, abin da ke nan ya sa ta soke hukuncin da kotun baya ta yanke ta kuma tabbatar da soke gabatar da jawabin. Majalisar Ƙasa ta Faransa ta tabbatar da wani hukunci da ya soke wani jawabi a wata jami'a a birnin Paris da aka shirya Rima Hassan za ta gabatar, wacce 'yar majalisar Tarayyar Turai ce kuma 'yar asalin Falasɗinu daga jam'iyyar Unyielding France (LFI). Ba wannan ne karon farko da aka soke jawabin da Rima Hassan za ta gabatar ba.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Kai-tsaye: Ƙungiyar WCK ta dakatar da aiki a Gaza bayan mummunan harin Isra'il a kan ma'aikatanta
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 422 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,382 da jikkata fiye da mutum 105,142. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara. 2041 GMT — ƙungiyar samar da abinci ta World Ce...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 422 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,382 da jikkata fiye da mutum 105,142. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara. 2041 GMT — ƙungiyar samar da abinci ta World Ce...
