Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 220, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 35,034 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,755 ne suka jikkata. 0901 GMT — 'Tsarin lafiyar Gaza zai rushe nan da awanni kaɗan saboda rashin fetur' Ma’aikatar lafiya na Falasdinawa a Gaza tace nan da ‘yan sa’o’i kadan tsarin kula da lafiya na yankin zai durƙushe, bayan yakin da ake yi ya hana shigar da man fetur yankin ta hanyar muhimman iyakoki. “’Yan sa’o’i ne suka rage mana kafin tsarin kula da lafiyar a Zirin Gaza ya durkushe, saboda babu man fetur din da ake bukata don kunna injin samar da wutar lantarki a asibitoci da motocin daukar marasa lafiya da motocin daukar ma’aikata,” a cewar Ma’aikatar Lafiya cikin wata sanarwa. 0727 GMT — Isra'ila ta kashe ma'aikatan lafiya sama da 500 a Gaza tun bayan soma yaƙi Akalla ma'aikatan kiwon lafiya 500 ne aka kashe tun farkon yakin da Isra’ila ta kaddamar kan Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta bayyana a daidai lokacin da ake bikin ranar ma’aikatan jinya ta duniya. Ma’aikatar ta lafiya ta bayyana cewa sojojin na Isra’ila sun kashe malaman jinya 138 a wannan yaƙi. Sannan akwai wasu ma’aikatan lafiyan 1500 da aka jikkata da kuma kama 312. 0630 GMT — Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari kan wurare uku na Hezbollah a kudancin Lebanon Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa jiragen yakinta sun kai hari kan wasu wurare uku na kungiyar Hizbullah a kudancin kasar Lebanon. “Jiragen sojin sama sun yi ruwan bama-bamai a wasu wuraren harba makamai masu linzami na Hezbollah a kauyukan Helta da Al-Hamam da kuma lalata ababen more rayuwa mallakar kungiyar a yankin Khraibeh. Tun da farko a ranar Lahadin da ta gabata, Hezbollah ta ce ta kai hari da wasu sabbin makamai masu linzami a kan wani wurin ajiye sojojin Isra'ila a kusa da yankin Zabdine a cikin gonakin Shebaa na Lebanon da suka mamaye.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Kai-tsaye: 'Tsarin lafiyar Gaza zai rushe nan da awanni kaɗan saboda rashin fetur'
Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 220, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 35,034 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,755 ne suka jikkata. 0901 GMT — 'Tsarin lafiyar Gaza zai rushe nan da awanni kaɗan saboda rashin fetur' Ma’aikata...

A taƙaice
Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 220, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 35,034 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,755 ne suka jikkata. 0901 GMT — 'Tsarin lafiyar Gaza zai rushe nan da awanni kaɗan saboda rashin fetur' Ma’aikata...
