Isra'ila ta kwashe kwana 210 tana yaƙi a Gaza, abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 34,622 — kashi 70 jarirai ne da ƙananan yara da mata — sannan suka jikkata fiye da mutum 77,867 kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0927 GMT — Tawagar Hamas na hanyar Masar domin tattaunawar sulhu Ƙungiyar Hamas ta sanar da cewa tawagarta na kan hanyar zuwa birnin Alkahira na Masar domin tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta, a daidai lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke gargaɗin cewa barazanar da Isra'ila ke yi na afka wa Rafah kan iya jawo "zubar jini". Masu shiga tsakani na ƙasashen waje na ta jiran ƙungiyoyin Falasɗinu su mayar da martani dangane da buƙatar tsagaita wuta tsawon kwanaki 40 domin musayar fursunoni. Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken shi ma ya ƙara jaddada matsayar Amurka kan rashin amincewa da batun afka wa Rafah, inda ya ce Isra'ila ba ta gabatar da wani tsari na kare farar hula ba da ke neman mafaka a can ba.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
KAI-TSAYE: Tawagar Hamas na hanyar Masar domin tattaunawar sulhu
Isra'ila ta kwashe kwana 210 tana yaƙi a Gaza, abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 34,622 — kashi 70 jarirai ne da ƙananan yara da mata — sannan suka jikkata fiye da mutum 77,867 kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0927 GMT — Tawagar Hamas na hanyar Masar domin...

At a glance