Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya isa kwana na 427 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,532 tare da jikkata mutum fiye da 105,800. A Lebanon, Isra'ila ta amince ta tsagaita wuta bayan ta kashe fiye da mutum 4,047 tun daga Oktoban 2023. 0617 GMT — Rundunar Sojin Isra'ila ta yi wa asibitin Kamal Adwan da ke Beit Lahia a arewacin Gaza ƙawanya inda suke ci gaba da buɗe wuta tare da toshe duka hanyoyin da ke zuwa asibitin, kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya bayyana. Motocin soji na tunkafrar asibitin inda suke tafe suna ɓarin wuta inda ake jin ɓarin wutar daga ko ina da ke makwabtaka da asibitin. Isra'ila ta kaddamar da wani gagarumin farmaki ta kasa a arewacin Gaza tun ranar 5 ga watan Oktoba domin "hana" kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas sake haduwa. 0046 GMT — Isra’ila ta ƙwace kadada 5,930 ta filaye a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan Isra’ila ta sanar da ƙwace kadada 5,930 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, inda ta ayyana wurin da ta ƙwace a matsayin mallakarta da zummar faɗaɗa matsugunan ‘yan kama wuri zauna. Kamar yada kafar watsa labaran Isra’ila ta Channel 14 ta bayyana, hukumomin Isra’ila ƙarƙashin jagorancin ministan kuɗi Bezalel Smotrich ya sanar da wannan matakin a abin da ya kira ɗaya daga cikin faɗaɗa ƙasar mafi girma a tsawon shekaru.
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Kai-tsaye: Sojojin Isra'ila sun yi wa asibitin Kamal Adwan da ke Gaza ƙawanya
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya isa kwana na 427 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,532 tare da jikkata mutum fiye da 105,800. A Lebanon, Isra'ila ta amince ta tsagaita wuta bayan ta kashe fiye da mutum 4,047 tun daga Oktoban 2023. 0617 GMT — Rundunar Sojin Isra'ila ta yi wa asibitin Ka...

Em resumo
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya isa kwana na 427 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,532 tare da jikkata mutum fiye da 105,800. A Lebanon, Isra'ila ta amince ta tsagaita wuta bayan ta kashe fiye da mutum 4,047 tun daga Oktoban 2023. 0617 GMT — Rundunar Sojin Isra'ila ta yi wa asibitin Ka...
