Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Kai-tsaye: Sojojin Isra'ila sun sace Falasɗinawa 300 daga asibitin Gaza

Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 166 - ya kashe Falasdinawa akalla 31,819 tare da raunata wasu 73,934 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki. 0019 GMT — Sojojin Isra'ila sun sace Falasɗina...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:13
Kai-tsaye: Sojojin Isra'ila sun sace Falasɗinawa 300 daga asibitin Gaza
Bu haberde ne var?

Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 166 - ya kashe Falasdinawa akalla 31,819 tare da raunata wasu 73,934 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki. 0019 GMT — Sojojin Isra'ila sun sace Falasɗina...

Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 166 - ya kashe Falasdinawa akalla 31,819 tare da raunata wasu 73,934 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki. 0019 GMT — Sojojin Isra'ila sun sace Falasɗinawa 300 daga asibitin Gaza Sojojin Isra'ila sun yi awon gaba da Falasɗdinawa kusan 300 a ci gaba da kutsawa da suke yi cikin asibitin Al Shifa da ke birnin Gaza. Wata sanarwa ta ce "sojoji sun kama kusan mutum 300 tare da kawar da ƴan ta'adda da dama Sojojin sun kai harin ne a ranar Litinin da ta gabata, wanda ke dauke da dubban marasa lafiya da suka jikkata da kuma mazauna wurin. A shekarar da ta gabata a watan Nuwamba, Isra'ila ta kai hari a asibitin, lamarin da ya tayar da hankalin kasashen duniya. Tel Aviv ta yi ikirarin karya cewa mayakan Hamas na amfani da asibitin wajen ayyukan soji. Kwanaki bayan haka ya bayyana a fili cewa sojojin Isra'ila a haƙiƙa suna magana ne a kan tudun da ke ƙarƙashin ginin da Isra'ila ta gina a shekarar 1983 a lokacin da ta yi wa Gaza mummunar mamayar. 0030 GMT — Shugabannin Amurka da Isra'ila za su gana a Washington Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant zai gana da sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin a mako mai zuwa a birnin Washington, kamar yadda wani jami'in tsaron Amurka ya tabbatar. Jami'in, wanda ya yi magana da sharadin sakaya sunansa don bayar da cikakkun bayanai da ba a bayyana ba tukuna, ya ce Austin da Gallant suna shirin tattaunawa don ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su, da kai taimakon jinƙai ga Gaza da kuma kare wadanda ke Rafah. Sama da mutum miliyan daya da suka rasa matsugunansu suna samun mafaka a kudancin birnin Gaza, inda Isra’ila ta ce tana shirin kai farmaki ta kasa.