Tsawon kwanaki 103, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,285 da raunata mutum 61,154. 1246 GMT — Sojojin Isra’ila sun lalata makabarta, sun tono gawawwaki a Khan Younis Janyewar sojojin Isra’ila daga yankunan birnin Khan Younis ya nuna irin barnar da sojojin suka yi a makabartar inda suka tona kaburbura da dama. Wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ce sojojin na Isra’ila sun janye da safiyar Litinin inda suka bar yankin da asibitin Khan Younis Nasser yake. Ya bayyana cewa sojojin sun lalata makabartar tare da tono kaburbura tare da amfani da buldoza domin lalata wasu wurare a cikin makabartar. 1120 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa uku kusa da sansanin ƴan gudun hijira na Balata Akalla Falasɗinawa uku harin Isra’ila ta kashe a wani hari ta sama da sojojinta suka kai a cikin wata mota a a kua da sansanin ƴan gudun hijira na Balata da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya tabbatar. Kungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent ta bayyanacewa ta yi kokari ta kai dauki bayan dakarun na Isra’ila sun janye daga wurin inda suka gano gawarwakin matasan. Zuwa yanzu Isra’ila ta kashe sama da mutum 24,000 a Gaza. 0825 GMT — 'Yan sandan Isra'ila sun tarwatsa zanga-zangar Yahudawa masu adawa da yakin Gaza ‘Yan sandan Isra’ila sun tarwatsa wata zanga-zanga da aka gudanar a birnin Tel Aviv na Isra’ila inda masu zanga-zangar ke nuna rashin goyon bayansu kan yakin da sojojin kasar ke ci gaba da yi a Gaza. Jaridar Haaretz daily ta ruwaito cewa ‘yan sanda sun yi amfani da karfi domin murkushe masu zanga-zangar inda suka yi ikirarin cewa zanga-zangar “tana cutar da tunanin jama'a.” ‘Yan sandan sun yi ikirarin cewa taron an yi shi ne ba bisa ka’ida ba inda aka ga ‘yan sandan suna kwace tutocin masu zanga-zangar. 0745 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 13 a Khan Younis Akalla Falasdinawa 13 Isra’ila ta kashe a hare-haren da ta kai Khan Younis da ke kudancin Gaza, kamar yadda wani rahoto ya bayyana. Bayan haka akwai kuma wasu gomman Falasdinawan da suka samu rauni a hare-hare ta sama da kasa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasdinu WAFA ya tabbatar. Haka kuma ya ce jiragen yakin na Isra’ila sun kai hari kan gidajen Falasdinawa a yammacin Khan Younis.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
KAI-TSAYE: Sojojin Isra’ila sun lalata makabarta, sun tono gawawwaki a Khan Younis
Tsawon kwanaki 103, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,285 da raunata mutum 61,154. 1246 GMT — Sojojin Isra’ila sun lalata makabarta, sun tono gawawwaki a Khan Y...

Tsawon kwanaki 103, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,285 da raunata mutum 61,154. 1246 GMT — Sojojin Isra’ila sun lalata makabarta, sun tono gawawwaki a Khan Y...
