الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: Sojojin Isra'ila sun kasa mamayar ko da ƙauye ɗaya a Lebanon — Hezbollah

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 402 — ya kashe akalla Falasdinawa 43,603 da jikkata 102,929, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,136 tun Oktoban bara. Litinin, 11 ga watan Nuwamban 2024 0925 GMT — Rund...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: Sojojin Isra'ila sun kasa mamayar ko da ƙauye ɗaya a Lebanon — Hezbollah
لمحة سريعة

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 402 — ya kashe akalla Falasdinawa 43,603 da jikkata 102,929, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,136 tun Oktoban bara. Litinin, 11 ga watan Nuwamban 2024 0925 GMT — Rund...

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 402 — ya kashe akalla Falasdinawa 43,603 da jikkata 102,929, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,136 tun Oktoban bara. Litinin, 11 ga watan Nuwamban 2024 0925 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta kasa mamayar ko da ƙauye ɗaya a Lebanon tun bayan da ta fara kai hare-harenta cikin ƙasar a watan Satumba, a cewar ƙungiyar Hezbollah. "Bayan shafe kwana 45 ana mummunan yaƙi, har yanzu maƙiya sun kasa mamayar ko da ƙauye ɗaya a ƙasar Lebanon," kamar yadda mai magana da yawun ƙungiyar Hezbollah, Mohammad Afif ya shai da taron manema labarai a kudancin Beirut, inda Isra'ila ke ta kai hare-haren sama a wajen. Ƙarin labarai ???? 0044 GMT — Kungiyar Euro-Med ta buƙaci MDD ta ayyana yunwa a arewacin Gaza Kungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Euro-Med ta buƙaci kungiyoyin kasa da kasa da na Majalisar Dinkin Duniya da su ayyana a hukumance cewa ana fama da yunwa a arewacin Gaza, inda aka hana agaji da kayayyaki isa ga dubban mazauna yankin sama da kwanaki 50. Bisa la'akari da cewa Isra'ila ta hana shigar da kayayyaki da kayan agaji ga dubban mazauna yankin arewacin Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya sama da kwanaki 50 a yanzu, dole ne hukumomin kasa da kasa da na Majalisar Dinkin Duniya da abin ya shafa su ayyana yunwa a yankin." Kungiyar ta ce a cikin wata sanarwa daga hedkwatar ta Geneva. Ta ƙara da cewa, amfani da yunwa a matsayin makami daya ne daga cikin ayyukan kisan gillar da Isra'ila ke ci gaba da yi a Zirin Gaza, wanda ya hada da kashe-kashen jama'a da gudun hijira. 0058 GMT — Masar da Malaysia sun amince su yi aiki tare don cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Lebanon Shugaban ƙasar Masar Abdel Fattah el Sisi ya sanar da cewa shi da firaministan Malaysia Anwar Ibrahim suna da aniya irin ɗaya ta yin aiki tare don cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Gaza na Falasɗinu da kuma Lebanon. Tattaunawar da ta haɗa da batutuwan yanki da na ƙasashen duniya, inda shugabannin biyu suke jaddada buƙatar ci gaba da ƙoƙarin ganin an dakatar da rikici a Gaza da Lebanon da kuma ba da damar shigar da kayayyakin agaji cikin yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya.