Yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ta shiga kwana na 22 a yau. Rahotanni sun ce yaƙin ya kashe fiye da Falasɗinawa 48,180, inda a yanzu aka sauya zuwa 62,000 saboda an ayyana wadanda suka ɓata a matsayin sun mutu. Lahadi, 9 ga Fabrairun 2025 0717 GMT — Sojojin Isra'ila sun fara janyewa daga Netzarim da ke Gaza a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Hamas. Kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa sojojin sun fara janyewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Gaza. Hoton tauraron ɗan’adam ya kuma nuna yadda Netzarim yake a yanzu, wani yanki na tsakiyar Gaza da sojojin Isra'ila suka fatattaki mutane bayan mamaye shi a ranar 20 ga Agusta, 2024. 0317 GMT — Jami'an diflomasiyyan Pakistan da Iran sun yi watsi da aniyar Trump kan Gaza Manyan jami'an diflomasiyya daga Pakistan da Iran sun tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya tare da mayar da hankali kan yankin Gaza na Falasdinu, inda suka yi watsi da shawarar shugaban Amurka Donald Trump na raba Falasdinawa da zama abin damuwa da rashin adalci a cewar wata sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Islamabad ta fitar. Ministan Harkokin Wajen Pakistan Ishaq Dar ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Iran Abbas Araghchi, inda suka tattauna halin da Falasdinawa ke ciki a Gaza. Da yake tsokaci kan shawarar Trump, Dar, wanda ke rike da mukamin mataimakin firaministan kasar, ya jaddada cewa kasar Falasdinu ta al'ummar Falasdinu ce, kuma hanya daya tilo da za ta dace kuma mai adalci ita ce samar da kasashe biyu, karkashin kudurorin kwamitin sulhu na MDD.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Kai-tsaye: Sojojin Isra'ila sun fara janyewa daga Netzarim da ke Gaza
Yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ta shiga kwana na 22 a yau. Rahotanni sun ce yaƙin ya kashe fiye da Falasɗinawa 48,180, inda a yanzu aka sauya zuwa 62,000 saboda an ayyana wadanda suka ɓata a matsayin sun mutu. Lahadi, 9 ga Fabrairun 2025 0717 GMT — Sojojin Isra'ila su...

At a glance
Yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ta shiga kwana na 22 a yau. Rahotanni sun ce yaƙin ya kashe fiye da Falasɗinawa 48,180, inda a yanzu aka sauya zuwa 62,000 saboda an ayyana wadanda suka ɓata a matsayin sun mutu. Lahadi, 9 ga Fabrairun 2025 0717 GMT — Sojojin Isra'ila su...
