Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 326, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,435— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,534, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Talata, 27 ga watan Agusta, 2024 2020 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla shida a Birnin Gaza na yankin Falasɗinu bayan jiragen yaƙinta sun kai hari wani gida. Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari a sansanin 'yan gudun hijira na Maghazi, inda suka kashe Falasɗinawa aƙalla uku, ciki har da jariri, tare da jikkata wasu, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasɗinu WAFA. Ya ƙara da cewa jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa sun gano gawa uku tare da mutanen da suka jikkata bayan Isra'ila ta yi luguden wuta a wani gida na iyalan Na'san a Layin Yermouk na Birnin Gaza. 2128 GMT — 'Yan kama-wuri-zauna sun kashe Bafalasɗine a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan 'Yan kama-wuri-zauna sun kashe wani Bafalasɗine tare da jikkata wasu uku a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, in ji Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasɗinu — a hare-hare fiye da 1,270 da 'yan ta'adda masu tsananin kishin kafa ƙasar Isra'ila suka ƙaddamar a kan Falasɗinawa tun watan Oktoban da ya gabata. Sojojin Isra'ila da da Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna sun kashe Falasɗinawa aƙalla 680 sannan suka jikkata kusan 6,000 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. Amurka da wasu ƙasashen Tarayyar Turai sun sanya takunkumai kan 'yan kama-wuri-zauna masu tayar da hanklai sannan sun sha yin kira ga Isra'ila ta hana su kai hare-hare kan Falasɗinawa. Sai dai hakan bai hana 'yan kama-wuri-zauna da masu kare su ci gaba da kashe Falasɗinawa ba. Gwamnatin Isra'ila cike take da shugabannin Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna da kuma masu tsananin kishin kafa ƙasar Isra'ila, waɗanda suka kafa rundunar mayaƙan sa-kai a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudus.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Kai-tsaye: Sojojin Isra'ila da Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna sun kashe Falasɗinawa
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 326, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,435— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,534, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Talata, 27 ga watan Agusta, 2024 2020 GMT — Isra'ila ta ka...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 326, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,435— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,534, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Talata, 27 ga watan Agusta, 2024 2020 GMT — Isra'ila ta ka...
