Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 200 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 34,151 tare da jikkata mutum sama da 77,084 a yayin da aka gano manyan ƙaburbura cike da gawawwaki, yawancinsu mata da ƙananan yara. 0330 GMT — Sojin ruwan Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a Gaɓar Tekun Gaza da kai hare-hare ta sama a arewacin ƙasar Jiragen yakin sojin Isra'ila sun kai hari a Gabar Tekun Al Zawaida da Deir al Balah, da Al Nusairat yayin da yankunan arewacin Gaza suka fuskanci hare-haren wuce gona da iri, wanda ya yi sanadiyar hallaka da jikkata wasu fararen hula, tare da lalata gidaje da kadarori, kamar yadda kafar yada labaran Falasdinu ta ce. Wakilan kamfanin dillancin labarai na WAFA sun ruwaito cewa, bayan shafe kwanaki 200 na hare-haren Isra'ila, jiragen yakin sojojin Isra'ila sun yi luguden wuta a Gabar Tekun Al Zawaida da Deir al Balah da ke tsakiyar Gaza a safiyar yau Talata. Hakazalika jiragen yakin sojin Isra'ila sun yi luguden wuta kan Gabar Tekun Al Nusairat. Sojojin Isra'ila sun kai hari a arewacin sansanin Al Nusairat da ke tsakiyar Gaza, yayin da jiragen yakin suka kai farmaki kan titin Thirty Streer da ke tsakiyar birnin. 2200 GMT — UNRWA ta yaba da nazari mai zaman kansa wanda ya ƙaryata ikirarin Isra'ila Hukumar da ke kula da ayyukan jinƙai na Falasɗinawa masu gudun hijira ta MDD, UNRWA ta yi maraba da sakamakon wani nazari mai zaman kansa kan yadda kungiyar ke bin ƙa’idar ba da ‘yancin kai da tsohuwar ministar harkokin kasashen Turai da harkokin waje, Catherine Colonna ta yi, wanda ya tabbatar da cewa kungiyar na da tsare-tsare don magance zarge-zargen da ake yi na nuna bacin rai. "Muna maraba da sakamakon binciken mai zaman kansa na UNRWA da @MinColonna ta yi. Ya nuna cewa muna da tsarin kiyaye dokokinmu - da muhimmiyar ka'idar jinƙai - kuma muna yin aiki lokacin da aka samu sabani," in ji kungiyar a shafin X. "Wannan yana da mahimmanci ga ayyukan agajin da muke yi a Gaza da kuma ayyukanmu a fadin yankin." Shugaban hukumar @UNRWA, Philippe Lazzarini, shi ma ya yi maraba da sakamakon nazarin sannan ya kara da cewa za su aiwatar da shawarwarin ba tare da ɓata lokaci ba. "Wannan zai karfafa kokarinmu da mayar da martani a lokacin daya daga cikin mawuyacin lokaci a tarihin al'ummar Falasdinu," in ji shi a X.
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Kai-tsaye: Sojin ruwan Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a Gaɓar Tekun Gaza da kai hare-hare ta sama a arewacin ƙasar
Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 200 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 34,151 tare da jikkata mutum sama da 77,084 a yayin da aka gano manyan ƙaburbura cike da gawawwaki, yawancinsu mata da ƙananan yara. 0330 GMT — Sojin ruwan Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a Gaɓar Tekun...

Bu haberde ne var?
Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 200 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 34,151 tare da jikkata mutum sama da 77,084 a yayin da aka gano manyan ƙaburbura cike da gawawwaki, yawancinsu mata da ƙananan yara. 0330 GMT — Sojin ruwan Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a Gaɓar Tekun...
