Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0332 GMT — Shugaban Hamas ya ce an kusa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila a Gaza Shugaban Hamas Isma'il Haniyeh ya ce ƙungiyar gwagwarmayarsa na gab da cimma yarjejeniyar sulhu da Isra'ila, a cewar wata sanarwa da aka wallafa ta kafar Telegram. "Ana gab da cimma yarjejeniya kan sulhu," in ji Haniyeh, a cewar sanarwar Masu shiga tsakani sun yi ta ƙoƙarin ƙulla yarjejeniya don ba da damar sakin kusan fursunoni 240 da aka yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoba, a lokacin harin da aka kai wa Isra'ila mafi muni a tarihinta. Mayakan Hamas sun kuma kashe mutum kusan 1,200 a harin da suka kai kan iyaka. Isra'ila ta kaddamar da hare-haren bama-bamai ba tare da bata lokaci ba tare da kai farmaki ta kasa a matsayin ramuwar gayya kan harin, inda ta lashi takobin rusa Hamas tare da ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su. 0117 GMT — Jami'in WHO ya ce halin da asibitin Gaza ke ciki ya zama 'bala'i' Wani babban jami'in Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ya bayyana halin da ake ciki a asibiti a Gaza a matsayin "mummunan bala'i", yana mai cewa yawanci ba sa aiki kuma abin da ya rage zai iya durkushewa sakamakon dubban haihuwar da ake sa ran mata za su yi a wata mai zuwa. Bayanin na Majalisar Dinkin Duniya ya zo ne sa'o'i kadan bayan da wani hari da aka kai ya shafi hawa na biyu na wani asibiti a arewacin Gaza, inda ya kashe mutum 12, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Gaza da kuma wani ma'aikacin lafiya.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
KAI TSAYE: Shugaban Hamas ya ce an kusa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila a Gaza
Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0332 GMT — Shugaban Hamas ya ce an kusa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da I...

At a glance
Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0332 GMT — Shugaban Hamas ya ce an kusa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da I...
