Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kai-tsaye: Shugaban China Xi Jinping ya yi kira da a gudanar da taron zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu

Isra'ila ta kashe akalla Falasdinawa 36,171 - kashi 71% daga cikinsu mata ne da yara da jarirai - tare da raunata 81,420 a yakin da ta kwashe kwanaki 237 tana yi a Gaza, in ji jami'an Falasdinawa. 0330 GMT — Shugaban China Xi Jinping ya yi kira da a gudanar da taron zaman lafiya tsakanin Isra'ila...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
Kai-tsaye: Shugaban China Xi Jinping ya yi kira da a gudanar da taron zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu
A taƙaice

Isra'ila ta kashe akalla Falasdinawa 36,171 - kashi 71% daga cikinsu mata ne da yara da jarirai - tare da raunata 81,420 a yakin da ta kwashe kwanaki 237 tana yi a Gaza, in ji jami'an Falasdinawa. 0330 GMT — Shugaban China Xi Jinping ya yi kira da a gudanar da taron zaman lafiya tsakanin Isra'ila...

Isra'ila ta kashe akalla Falasdinawa 36,171 - kashi 71% daga cikinsu mata ne da yara da jarirai - tare da raunata 81,420 a yakin da ta kwashe kwanaki 237 tana yi a Gaza, in ji jami'an Falasdinawa. 0330 GMT — Shugaban China Xi Jinping ya yi kira da a gudanar da taron zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kira taron zaman lafiya game da yakin da Isra'ila ke yi kan Gaza da ta yi wa kawanya a lokacin da yake jawabi ga shugabannin kasashen Larabawa da jami'an diflomasiyya a wani dandalin tattaunawa a birnin Beijing. A wannan makon ne kasar Sin za ta karbi bakuncin shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi da wasu shugabannin kasashen Larabawa da dama, domin halartar wani taron tattaunawa kan yakin Gaza. Da yake jawabi ga tawagogin a safiyar ranar Alhamis, Xi ya ce, kasar Sin tana goyon bayan wani babban taro na zaman lafiya domin warware rikici. Xi ya ce "Gabas ta Tsakiya yanki ne da ake yi wa kyakkyawan fata na samun ci gaba, amma har yanzu yaƙi yana ci gaba da ruruwa a can." Ya kara da cewa "Bai kamata a ci gaba da yaki ba har abada. Bai kamata a ce an kasa yin adalco ba har abada." Xi ya kuma ce, China tana goyon bayan kasancewar Falasdinu cikakkiyar mamba a MDD, kuma tana goyon bayan babban taron zaman lafiya na kasa da kasa mai tushe, mai iko da inganci. China, wadda ke da kyakkyawar alaka da Isra'ila, ta sha gabatar da shawarwarin samar da kasashe biyu na warware rikicin Isra'ila da Falasdinu tsawon shekaru da dama. 2130 GMT — An kori ma'aikaciyar jinyar da aka bai wa lambar yabo kan tausayi bayan yin magana game da kisan kare dangi a Gaza Wani asibitin birnin New York ya kori wata ma’aikaciyar jinya bayan da ta yi nuni da yakin da Isra’ila ke yi a Gaza a matsayin kisan kiyashi a lokacin da take jawabin karbar lambar yabo. Ma’aikaciyar jinya da haihuwa Hesen Jabr, ‘Ba'amurkiya kuma Bafalasdiniya ce, wadda hukumar lafiya ta NYU Langone ta karrama ta saboda tausayin da take nunawa wajen kula da iyaye mata da suka rasa jariransu, take kuma alaƙanta aikinta da wahalar da iyaye mata ke sha a Gaza. Jabr ta ce, "Na ji zafi ganin yadda matan kasata ke tafka asara da ba za a iya misaltawa ba, a lokacin da ake yin kisan kare dangi a Gaza," in ji Jabr, a cikin wani bidiyo na jawabin da ta yi ranar 7 ga Mayu da ta wallafa a shafukan sada zumunta. "Wannan lambar yabo mai karfi ce a gare ni saboda waɗannan dalilai." Jabr ta rubuta a shafinta na Instagram cewa ta isa wurin aiki a ranar 22 ga Mayu don komawarta ta farko bayan samun lambar yabo lokacin da aka gayyace ta wata ganawa da shugaban asibitin da mataimakin shugaban ma'aikatan jinya "don tattauna yadda na sanya wasu cikin haɗari" da yadda "na lalata bikin karramawar" da "ɓata wa mutane rai" saboda a jawabina na nuna 'yar girmamawa ga iyaye mata 'yan kasata da ke cikin bakin ciki a kasata." Ta rubuta cewa bayan da ta yi aiki na dan lokaci sai aka sake kiran ta zuwa wani ofishi inda aka karanta takardar dakatar da ita sannan aka fitar da ita daga asibitin.