Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

KAI-TSAYE: Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta aika da jirgin ruwan nukiliya Gabas ta Tsakiya

Wannan shafi ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0600 GMT — Sarkin Jordan ya ce an wurga 'magunguna na bukatun gaggawa' a Gaza Ji...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:13
KAI-TSAYE: Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta aika da jirgin ruwan nukiliya Gabas ta Tsakiya
At a glance

Wannan shafi ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0600 GMT — Sarkin Jordan ya ce an wurga 'magunguna na bukatun gaggawa' a Gaza Ji...

Wannan shafi ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0600 GMT — Sarkin Jordan ya ce an wurga 'magunguna na bukatun gaggawa' a Gaza Jiragen sojin saman Jordan sun wuwwurga magunguna da ake bukata cikin gaggawa a asibitocin tafi-da-gidanka da ke yankin Gaza da aka mamaye, a cewar Sarki Abdullah II da safiyar Litinin. "Sojojin samanmu marasa tsoro sun jefa magunguna da ake bukata cikin gaggawa a asibitin wucin-gadi na Jordan da ke Gaza," in ji sarkin a sakon da ya wallafa a shafin X. 0534 GMT — Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta aika da jirgin ruwan nukiliya Gabas ta Tsakiya Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta ce aika da jirgin ruwan nukiliya yankin Gabas ta Tsakiya. “Ranar 5 ga watan Nuwamba, jirgin ruwa samfurin Ohio-class ya isa yankin da ke karkashi ikon Amurka,” in ji sanarwar da Cibiyar Tsare-Tsare ta Amurka (CENTCOM) ta wallafa a shafin X. Amurka ta aika da jirage biyu yankin Gabas ta Tsakiya tun daga ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta kaddamar da farmakin Operation Al Aqsa Flood a Isra'ila. 0400 GMT — Adadin mutanen da suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila ya kai 9,770 Ma'aikatar Kiwon Lafiya a Gaza ta ce ya zuwa ranar Lahadi mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila take kaiwa a Zirin Gaza sun kai 9,770. “Mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila a Zirin Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba sun kai 9,770, cikinsu har da kananan yara 4,800 da mata 2,550,” in ji sanarwar da ma'aikatar ta fitar. Ta kara da cewa a cikin awa 24 da suka wuce Isra'ila ta kashe Falasdinawa 270. A cikin awa 24 da suka wuce Isra'ila ta kashe Falasdinawa 270, a cewar sanarwar ma'aikatar lafiya ta Gaza./Hoto: AA