Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kai-tsaye: Qatar ta ce tattaunawar tsagaita wuta a Gaza ta kai wani muhimmin mataki

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwanaki 315 yanzu, ya kashe a kalla Falasdinawa 40,005 akasari mata da kananan yara tare da jikkata mutum fiye da 92,401, an ƙiyasta mutane 10,000 na binne a karkashin baraguzan gine-ginen da aka kai musu hari. Juma'a 16 ga Agustan 2024 0845 GMT — Firaminis...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
Kai-tsaye: Qatar ta ce tattaunawar tsagaita wuta a Gaza ta kai wani muhimmin mataki
A taƙaice

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwanaki 315 yanzu, ya kashe a kalla Falasdinawa 40,005 akasari mata da kananan yara tare da jikkata mutum fiye da 92,401, an ƙiyasta mutane 10,000 na binne a karkashin baraguzan gine-ginen da aka kai musu hari. Juma'a 16 ga Agustan 2024 0845 GMT — Firaminis...

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwanaki 315 yanzu, ya kashe a kalla Falasdinawa 40,005 akasari mata da kananan yara tare da jikkata mutum fiye da 92,401, an ƙiyasta mutane 10,000 na binne a karkashin baraguzan gine-ginen da aka kai musu hari. Juma'a 16 ga Agustan 2024 0845 GMT — Firaministan Qatar kuma Ministan Harkokin Wajen ƙasar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani ya ce tattaunawar shiga tsakani don aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza ta cimma mataki mai muhimmanci a tattaunawar da ya yi da takwaransa na riƙon ƙwarya na Iran Ali Bagheri Kani, wanda ya jaddada buƙatar matsa wa Isra'ila ta dakatar da "kisan kare dangi" a kan Falasdinawa. "A cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da firaministan Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar, Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, mun tattauna kan sabbin laifukan gwamnatin Isra'ila a Gaza da kuma hanyoyin dakatar da su," in ji Kani a wata sanarwa bayan tattaunawar a ranar Juma'a. Kani ya ce sun tattauna kan sulhun da ake yi a Doha da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma yarjejeniyar yin garkuwa da su tsakanin Isra'ila da Hamas. "Al Thani yana ishara ne da taron da Qatar ta shirya game da shawarwarin tsagaita wuta, yana mai bayyana sakamakon wannan mataki na tattaunawar a matsayin mai muhimmanci," in ji jami'in na Iran. Sauran labarai???? 0842 GMT — Malaysia ta ceto Falasɗinawa 127 daga Gaza Malaysia ta yi nasarar kwashe Falasdinawa 127 daga Gaza, lamarin da ya kai su ga samun mafaka a kudu maso gabashin Asiya. Mutanen sun haɗa da maza da mata da ƙananan yara, kuma sun isa sansanin sojin sama na Subang a cikin wani jirgin sama na Royal Malaysian Air Force. Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim ne ya ƙaddamar da wannan aikin ceto, wanda ya sanar da yin aikin a lokacin wani gangamin hadin kai ga Falasdinu a Kuala Lumpur a ranar 4 ga watan Agusta. 0742 GMT — Sojojin Isra'ila sun ba da umarnin sake kwashe mutane a Gaza Sojojin Isra'ila sun ba da sabbin umarni na ficewa ga mazauna yankuna da dama na tsakiya da kuma kudancin Gaza wadanda sojojin suka ayyana a matsayin "yankin da ke da aminci". A cikin wata sanarwa da ta fitar, sojojin Isra'ila sun umarci mazauna yankunan arewacin Khan Younis da ke kudancin Gaza da kuma yankunan gabashin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza da su ƙaurace wa yankunan.