Isra'ila ta kwashe kwana 266 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,765 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,429, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 1105 GMT — Ofishin kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya ya 'damu matuka' kan tashin hankalin da ke ta'aazara tsakanin Lebanon da Isra'ila Ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya damu matuka dangane da rikicin da ke faruwa tsakanin Lebanon da Isra'ila. "Mun damu matuka game da lamarin - inda aka kashe daruruwan mutane, dubbai suka jikkata, wasu dubban kuma suka rasa muhallansu, tare da karin sa'insa masu sanya damuwa," in ji mai magana da yawun Ravina Shamdasan yayin amsa tambayar da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya yi masa. "Muna jaddada bukatar kwantar da tarzoma da kuma dakatar da tashin hankali," in ji Shamdasan. Ta buƙaci da a gudanar da cikakken bincike kan duk wani lamari da ya shafi kisan fararen hula, tana mai cewa "hakan na da muhimmanci." Ta kara da cewa ofishin kare hakkin bil'adama ya samu rahotanni masu "saka matukar damuwa" na yara da ma'aikatan jinya da 'yan jarida a cikin wadanda aka kashe. 1024 GMT — Sojojin Isra'ila sun kara kutsawa cikin kudanci da arewacin Gaza Sojojin Isra'ila sun sake kutsawa cikin yankuna biyu na arewaci da kudancin Gaza, kuma jami'an kiwon lafiyar Falasdinu sun ce harin tankokin yaki a Rafah ya kashe akalla mutum 11. Mazauna yankin da kafafen yada labarai na cikin gida sun ce tankokin yaki sun kara yin yamma zuwa unguwar Shakoush da ke Rafah, lamarin da ya tilasta wa dubban mutanen da suka rasa matsugunansu barin sansaninsu, suka nufi arewa zuwa Khan Younis da ke kusa. Wani mazaunin yankin, wanda ya yi magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ce wasu manyan katafiloli a yankin Shakoush na tara yashi domin tankunan yaƙin Isra'ila su samu tsayawa a baya. Ya ƙara da cewa, “Wasu iyalai suna zaune a yankin da aka kai farmakin, kuma a yanzu dakarun mamaya sun yi wa wajen ƙawanya. "Halin da ake ciki yana da matukar hadari kuma iyalai da yawa suna tafiya zuwa Khan Younis, har ma daga yankin Mawasi, saboda al'amura sun kasance marasa aminci a gare su," in ji mutumin, wanda ya koma arewa cikin dare. A gefe guda kuma, sojojin Isra'ila sun ci gaba da kai sabon farmaki a unguwar Shujaiya da ke arewacin Gaza, inda tankokin yaƙi suka kutsa wajen a ranar Alhamis.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Kai-tsaye: Ofishin kare hakkin ɗan'adam na MDD ya 'damu sosai' kan tashin hankalin da ke ta'aazara tsakanin Lebanon da Isra'ila
Isra'ila ta kwashe kwana 266 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,765 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,429, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 1105 GMT — Ofishin kare hakkin bil'adama na Majal...

لمحة سريعة
Isra'ila ta kwashe kwana 266 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,765 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,429, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 1105 GMT — Ofishin kare hakkin bil'adama na Majal...
