Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kai-tsaye: Netanyahu yana jawo tsaiko wajen kwashe yara marasa lafiya 150 daga Gaza zuwa UAE

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 297, inda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 39,363 - akasarinsu mata da yara. Ya kuma raunata mutum 90,923, an kuma yi ƙiyasin cewa sama da mutum 10,000 ke binne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine. 0935 GMT — Yawan Falasɗinawan da suka mutu a y...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
Kai-tsaye: Netanyahu yana jawo tsaiko wajen kwashe yara marasa lafiya 150 daga Gaza zuwa UAE
De un vistazo

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 297, inda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 39,363 - akasarinsu mata da yara. Ya kuma raunata mutum 90,923, an kuma yi ƙiyasin cewa sama da mutum 10,000 ke binne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine. 0935 GMT — Yawan Falasɗinawan da suka mutu a y...

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 297, inda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 39,363 - akasarinsu mata da yara. Ya kuma raunata mutum 90,923, an kuma yi ƙiyasin cewa sama da mutum 10,000 ke binne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine. 0935 GMT — Yawan Falasɗinawan da suka mutu a yaƙin Isra'ila a Gaza ya kai 39,363 Aƙalla Falasɗinawa 39,363 aka kashe a kusan tsawon wata 10 da a Isra'ila ta shafe tana yaƙi a Gaza, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinu da ke yankin da aka yi wa ƙawanya ta faɗa. Adadin waɗanda suka mutu ya haɗa da mutuwar mutum 39 a cikin sa'o'i 24, a cewar alkaluman ma'aikatar, wanda ya kuma bayyana mutum 90,923 da suka samu raunuka a Gaza tun lokacin da aka fara yaƙin a ranar 7 ga Oktoba, 2023. 0007 GMT –– Netanyahu yana jawo tsaiko wajen kwashe yara marasa lafiya 150 daga Gaza zuwa UAE Kamfanin dillancin labaran Isra''ila ya rawaito cewa firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya jinkirta kwashe kananan yara Falasdinawa 150 marasa lafiya da waɗanda suka jikkata daga Gaza zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa domin yi musu magani. A ranar Litinin ne ya kamata yara marasa lafiya daga Gaza su tashi zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa daga Isra'ila, amma bayan abin da ya faru a Majdal Shams, Firaiminista Netanyahu ya ba da umarnin a jinkirta tafiyarsu," in ji hukumar yada labaran kasar. Ta ce Netanyahu ya yanke shawarar ɗage tashin yaran ta filin jirgin saman Ramon na Isra'ila. Hukumar ta ba da sabuwar ranar tashi ga yara marasa lafiya. Kawo yanzu dai babu wani bayani daga UAE kan lamarin.