Tsawon kwanaki 109, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,295 da raunata mutum 63,000. 1125 GMT — Netanyahu ya ce Isra'ila za ta ƙara kutsawa Gaza bayan kashe mata sojoji 24 Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila za ta ci gaba da yaƙin da take yi a Gaza har sai "ta cimma nasara" duk da wahala mafi muni da ta fuskanta a ƴan kwanakin nan a yaƙin. "Jiya mun sha matuƙar wahalar da ba mu taɓa sha ba tun da aka fara yaƙin nan," in ji Netanyahu. "Ba za mu daina yaƙi ba har sai mun cimma nasara." Ya ce rundunar soji na "bincike kan bala'in da ya faru" inda aka kashe sojojin ƙsar 21 a lokacin da bam ya fashe a wani gini a tsakiyar Gaza, lamarin da ya jawo Isra'ila ta rasa soja 24 a cikin kwana guda kacal. 1029 GMT — Ana ci gaba da ƙoƙrin sasantawa a kan batun Gaza, in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Qatar Ana ci gaba da ƙoƙarin sasantawa don kawo ƙrshen yaƙin Isra'ila a Gaza, a cewar mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Qatar a wani taron manema labarai. Ya ƙara da cewa, ta'azzarar tashin hankalin da ake samu a Tekun Maliya alama ce ta "babban tashin hankali." Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da dakarun Birtaniya suka kai sabbin hare-haren sama a kan ƙungiyar Houthi da ake da alaƙa da Iran, waɗanda suke lalata harkokin kasuwancin jiragen ruwa don nuna adawarsu da yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza. 1117 GMT — Dakarun Hamas sun kashe sojojin Isra’ila 21 a harin kwanton-bauna Isra'ila na ci gaba da kai hari kan Falasdinawa a Gaza inda suke kashe mutane da dama a kullum. / Hoto: Reuters Sojojin Isra’ila a ranar Talata sun tabbatar da cewa akalla dakarunsu 21 Hamas ta kashe tare da raunata da dama a harin kwanton-ɓauna daya da aka kai musu a Zirin Gaza. A wata sanarwa, mai magana da yawun sojojin kasar Rear Adm. Daniel Hagari ya ce lamarin ya faru ne kusa da iyakar Kissufim a daidai lokacin da Hamas din suka kai hari kan sojojin. Ya bayyana cewa Hamas sun harba makamin roka kan wata tankar yaƙin Isra’ila inda kuma a lokacin wani tashin bam ya rusa wani gini mai hawa biyu.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
KAI-TSAYE: Netanyahu ya ce Isra'ila za ta ƙara kutsawa Gaza bayan kashe mata sojoji 24
Tsawon kwanaki 109, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,295 da raunata mutum 63,000. 1125 GMT — Netanyahu ya ce Isra'ila za ta ƙara kutsawa Gaza bayan kashe mata...

At a glance
Tsawon kwanaki 109, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,295 da raunata mutum 63,000. 1125 GMT — Netanyahu ya ce Isra'ila za ta ƙara kutsawa Gaza bayan kashe mata...
