Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 304, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,583 — galibinsu mata da yara — tare da jikkata mutum sama da 91,398. Litinin, 5 ga watan Agusta, 2024 0016 GMT — Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fito da sabbin sharuɗɗa a wanda ya ce dole a cika kafin ya amince da yarjejeniyar musayar fursunoni da ƙungiyar Hamas, ciki har da tursasa wa Falasɗinawa kusan 150 barin ƙasarsu har abada, a cewar kafofin watsa labarai na ƙasar. Ya ce dole ne a fitar da wasu Falasɗinawa daga ƙasarsu zuwa wasu ƙasashe bayan an sake su daga gidajen yarin Isra'ila, kamar yadda gidan talbijin na Channel 13 da ke Isra'ila ya ruwaito, inda ya ambato wasu majiyoyi da bai bayyana su ba. A cewar majiyoyin, fursunonin, waɗanda suka kusa 150, ana zarginsu da kashe Isra'ilawa. 0205 GMT — Shugabannin tsaron Amurka da na Isra'ila sun tattauna kan matakin Washington na tura kayan yaƙi Gabas ta Tsakiya Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin da takwaransa na Isra'ila Yoav Gallant sun tattauna kan tura kayan yaƙi zuwa Gabas ta Tsakiya a wayar tarho da suka yi ranar Lahadi. "Sun tattauna kan matsayin dakarun Amurka da matakin da Ma'aikatar Tsaro ta ɗauka na tura ƙarin matakan tsaro domin goyin bayan Isra'ila, da kuma yunƙurin hana ci gaba da tashin jijiyoyin wuya a yankin," in ji wata sanarwa da ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta fitar. Yayin tattaunawar tasu, Austin ya jaddada goyon bayan da Amurka take bai wa Isra'ila na kare ta "a kowane hali" da kuma 'yancin Isra'ila na mayar da martani kan barazana daga Iran, da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon da mayaƙan Houthi da ke Yemen.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Kai-tsaye: Netanyahu ya bijiro da sabbin sharuɗɗa kan musayar fursunoni a Gaza
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 304, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,583 — galibinsu mata da yara — tare da jikkata mutum sama da 91,398. Litinin, 5 ga watan Agusta, 2024 0016 GMT — Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fito da sabbin sharuɗɗa a wanda ya ce dole a c...

لمحة سريعة
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 304, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,583 — galibinsu mata da yara — tare da jikkata mutum sama da 91,398. Litinin, 5 ga watan Agusta, 2024 0016 GMT — Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fito da sabbin sharuɗɗa a wanda ya ce dole a c...
