Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 94 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 22,835 sannan suka jikkata mutum 58,416, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 1423 GMT — Netanyahu na son rufe wasu ma’aikatun Isra’ila don rage kashe kudi Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya soma tunanin kulle wasu ma’aikatun gwamnatin kasar a yunkurin rage kashe kudi, kamar yadda kafar watsa labarai ta kasar ta bayyana a ranar Litinin. Netanyahu na tunanin ci gaba da kasancewa da wasu ministoci a gwamnatinsa wadanda ba su da ma’aikatu, don guje wa rikicin kawancen da za a iya fuskanta, kamar yadda gidan rediyon Reshet Bet ya bayyana. Ana sa ran gudanar da taro na musamman a ranar Alhamis mai zuwa domin tattaunawa kan yiwuwar rufe wasu kananan ma’aikatun kasar 0644 GMT — Isra'ila ta kashe karin mutum 73 a Gaza cikin awa 24 Akalla Falasdinawa 73 ne suka mutu sannan 99 suka jikkata a Gaza sakamakon hare-haren da jiragen yakin Isra'ila suka kai cikin awanni 24, a cewar Ma'aikatar Kiwon Lafiyar yankin. Ranar Lahadi da tsakar dare, jiragen yakin Isra'ila sun kai hari a wani gida a birnin Khan Younis inda wadanda suka rasa matsugunansu suke zama, a cewar kamfanin dillancin labaran Wafa na Falasdinu. Ya ce an kashe fararen-hula akalla 12 tare da jikkata mutum 50. Kazalika jiragen yakin sun kai hari a wata makaranta ta Majalisar Dinkin Duniya wadda mutane suke samun mafaka asansanin 'yan gudun hijira na Al Maghazi da ke tsakiyar Gaza inda suka kashe fararen-hula hudu, ciki har da wata mace, in ji kamfanin dillancin na labarai. 0015 GMT — Babban jami'in sojin Isra'ila ya ce za su ci gaba da kai hari a Gaza a 2024 Babban jami'in sojin Isra'ila ya ce mai yiwuwa yakin da suke yi a Gaza zai ci gaba a daukacin shekarar da muka shiga. Shugaban Rundunar sojin Isra'ila Herzi Halevi ya yi bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara a Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, a cewar wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar. Ya ce shekarar 2024 za ta kasance mai "tsanani.” "Za mu ci gaba da yaki a Gaza. Za mu shafe wannan shekarar muna yaki a Gaza, wannan tabbas ne,” in ji shi. 2300 GMT — Mutum 6,000 da suka samu munanan raunuka na bukatar 'kulawar gaggawa' a kasashen waje Gwamnatin Gaza ta sanar cewa mutun 6,000 da suka samu munanan raunuka sakamakon hare-haen da Isra'ila take kai wa Gaza suna bukatar a fitar da su kasashen waje domin ba su kulawar gaggawa. A wata sanarwa da ofishin watsa labarai na Gaza ya fitar ya bayyana "babban bala'in" da fannin lafiya ya fada a cikin tun ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a yankin. Sanarwar ta ce asibitoci 30 a yankin sun daina aiki a yayin da aka jikkata fiye da mutum 58,000 sakamakon hare-hare. "Muna kira ga 'yan'uwanmu da ke Masar su yi gaggawar bude iyakar Rafah sannan su bari a fitar da mutum 6,000 daga Gaza wadanda suka samu munanan raunuka domin samun kulawar gaggawa saboda akwai karancin kayan aiki ga marasa lafiya a Gaza,” in ji sanarwar. Sanarwar Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta ce Isra'ila tana yunkurin durkusar da Asibitin Al Aqsa Martyrs da ke Deir Al Balah inda ta yi masa luguden wuta da jirage marasa matuka/ Hoto: AA 2100 GMT — Jirage marasa matuka na Isra'ila sun bude wuta a Asibitin Al Aqsa Martyrs — Ma'aikatar Lafiya Jirage marasa matuka na Isra'ila sun kai hare-hare a Asibitin Al Aqsa Martyrs da ke Tsakiyar Gaza, a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Lafiya ta yankin ta fitar. "Sojojin Isra'ila da ke mamaya sun yi amfani da jirage marasa matuka wurin kai hari kan marasa lafiya da ma'aikatan asibiti," in ji ma'aikatar ta lafiya. "Jiragen marasa matuka sun yi luguden wuta babu kakkautawa a kusa da gine-gine da yankunan da asibitin yake inda suke kai hari kan duk wani abu da suka ga yana motsi," sanarwar ta kara da cewa. Ta ce hare-haren sun jikkata marasa lafiya da sauran mutane inda ake tserewa daga asibitin yayin da jiragen ke bin mutane suna bude musu wuta. Yunkurin Isra'ila na ganin Asibitin Al Aqsa Martyrs ya daina aiki zai yi sanadin mutuwar dubban majinyata da ke cikinsa, in ji sanarwar. An kai mutanen da suka jikkata Asibitin Al Aqsa Martyrs bayan luguden wutar da Isra'ila ta yi a Deir Al Balah, Gaza ranar 7 ga watan Janairu, 2024. / Hoto: AA
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
KAI-TSAYE: Netanyahu na son rufe wasu ma’aikatun Isra’ila don rage kashe kudi
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 94 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 22,835 sannan suka jikkata mutum 58,416, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 1423 GMT — Netanyahu na son rufe wasu ma’aikatun Isra’ila don rage kashe kudi Fira...

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 94 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 22,835 sannan suka jikkata mutum 58,416, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 1423 GMT — Netanyahu na son rufe wasu ma’aikatun Isra’ila don rage kashe kudi Fira...
