Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Kai-tsaye: Netanyahu na Isra'ila ya ƙi amincewa da shirin Masar na tsagaita wuta a Gaza

Yakin kisan kare dangi na Isra'ila a Gaza - da ke cikin kwanaki 388 - ya kashe kusan mutum 43,000 da raunata fiye da 100,500, kuma ana fargabar mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum 2,672 tun daga Oktoban bara. Litinin 28 ga Oktoban 2024 2237 GMT — Firaministan I...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Netanyahu na Isra'ila ya ƙi amincewa da shirin Masar na tsagaita wuta a Gaza
Kwa muhtasari

Yakin kisan kare dangi na Isra'ila a Gaza - da ke cikin kwanaki 388 - ya kashe kusan mutum 43,000 da raunata fiye da 100,500, kuma ana fargabar mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum 2,672 tun daga Oktoban bara. Litinin 28 ga Oktoban 2024 2237 GMT — Firaministan I...

Yakin kisan kare dangi na Isra'ila a Gaza - da ke cikin kwanaki 388 - ya kashe kusan mutum 43,000 da raunata fiye da 100,500, kuma ana fargabar mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum 2,672 tun daga Oktoban bara. Litinin 28 ga Oktoban 2024 2237 GMT — Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da shirin da Masar ta gabatar na tsagaita wuta na wucin gadi a Gaza da aka yi wa ƙawanya. Duk da goyon bayan da akasarin ministocin Isra'ila suka yi kan shawarar Masar, Tel Aviv ta yanke shawarar yin watsi da yarjejeniyar ne saboda adawar Netanyahu, wanda ya jaddada cewa "za a yi tattaunawar ne kawai ana cikin yaƙin," a cewar tashar 12 ta Isra'ila. Ƙarin labarai ???? 2116 GMT — Adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila a Lebanon ya kai 2,672 Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai kan Lebanon tun daga ranar 8 ga watan Oktoban bara ya kai 2,672, tare da jikkata 12,468. Akalla mutum 19 ne suka mutu yayin da 108 suka jikkata a hare-haren da Isra'ila ta kai a kasar Lebanon a ranar Asabar, a cewar ma'aikatar. 2217 GMT — Al-Qassam ta ce ta kai hari kan motocin sojojin Isra'ila a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia Rundunar Qassam Brigades, reshen soja na kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta sanar da kai hari kan motocin sojin Isra'ila a arewacin Gaza. A cikin wata sanarwa da suka fitar ta kafar sadarwa ta Telegram sun ce, "Mun auna wani jirgin yakin Yahudawan masu tsaurin ra'ayin kafa ƙasar Isra'ila da wasu buldoza na sojan D9 guda biyu da bama-bamai a kusa da makabartar gabashin Jabalia." Bugu da ƙari, mayaƙan na Qassam sun kai hari kan tankar Merkava 4 ta Isra'ila tare da bama-baman Shawaz a kusa da tashar Nathr a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia. 2038 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 1,000 a arewacin Gaza cikin makonni 3 Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa sama da 1,000 a arewacin Gaza, tare da tilasta wa rabin al'ummar yankin tserewa daga hare-haren bama-bamai, yayin da sauran rabin suka maƙale ba tare da ruwa ko abinci ba kusan makonni uku, kamar yadda hukumar tsaron farar hula ta Falasdinu ta sanar. Mahmoud Bassal kakakin hukumar tsaron farar hula ta Falasdinu ya bayyana a cikin wani bidiyo da aka watsa a shafukan sada zumunta cewa sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa sama da 1,000 a hare-haren da suka kwashe tsawon makwanni uku suna kai wa a arewacin Gaza, wanda har yanzu ake ci gaba yi. “Fiye da Falasdinawa 100,000 a yankunan Jabalia da Beit Hanoun, da kuma Beit Lahia na fama da ƙawanya da ruwan bama-bamai da Isra’ila ke yi, yayin da sauran rabin al’ummar da suka kai kusan 200,000, aka tilasta musu yin gudun hijira zuwa birnin Gaza, mafi kusa da gwamnati zuwa arewa,” Bassal ya shaida wa Anadolu. Ya ci gaba da cewa: Sojojin Isra'ila suna kashe duk wanda ya yi kokarin ba da taimako ga Falasdinawan da suka maƙale a arewacin Zirin Gaza, wadanda ke fama da ƙarancin ruwa da magunguna, da abinci.