A yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 360, ta kashe Falasɗinawa fiye da 41,595. Kazalika, ta kashe fiye da mutum 800 tun da ta ƙaddamar da hare-hare a Lebanon ranar 23 ga watan Satumba. Litinin, 30 ga watan Satumba, 2024 0822 GMT — Mutum fiye da 100,000 sun tsere daga Lebanon zuwa Syria: MDD Mutum fiye da 100,000 sun tsere daga Lebanon zuwa Syria tun da rikici ya yi ƙamari tsakanin Isra'ila da Hezbollah a watan nan, a cewar shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya. Filippo Grandi ya wallafa saƙo a shafinsa na X cewa waɗanda suke tserewa sun haɗa da 'yan Lebanon da ’yan ƙasar Syria. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya tana taimaka wa mutanen da suka isa Syria, in ji shi. 0644 GMT — Isra'ila ta kashe shugabanni uku na Falasɗinawa a harin da ta kai tsakiyar Beirut Dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare ta sama da sanyin safiyar Litinin a yankin Kola na birnin Beirut, wanda ya kasance irinsa na farko da suka kai a cikin babban birnin na Lebanon tun da suka soma yaƙi da Hezbollah a watan Oktoban da ya wuce. Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito cewa jirgi mara matuƙi na Isra'ila ya kai hari a hawa na biyar na wani gida a kan hanyar da ta haɗa Beirut da Filin Jirin Saman Ƙasa da Ƙasa na Rafik Hariri. Harin ya tayar da gobara a gidan, ko da yake 'yan kwana-kwana sun kashe ta. Daga bisani ƙungiyar Popular Front for the Liberation of Palestine (PFLP) ta tabbatar da cewa harin ya kashe shugabanninta uku: Mohammed Abdel Aal, wani mamba na ɓangaren siyasarta kuma shugaban sashen soja da tsaro; Imad Ouda, kwamanda soji na Lebanon, da Abdel Rahman Abdel Aal, wanda ba a bayyana matsayinsa ba. Ma'aikatan kwana-kwana suna ƙoƙarin kashe gobarar da ta tashi bayan Isra'ila ta kai hari a wani gidan bene a yankin Kola na birnin Beirut, ranar 30 ga watan Satumba, 2024. / Hoto: AA 0554 GMT — Hamas ta tabbatar da kisan shugabanta a harin Isra'ila Ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa, Hamas, ta ce an kashe shugabanta na Lebanon Fateh Sherif Abu el-Amin tare da iyalansa a wani hari da Isra'ila ta kai a kudancin ƙasar.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Kai-tsaye: Mutum fiye da 100,000 sun tsere daga Lebanon zuwa Syria: MDD
A yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 360, ta kashe Falasɗinawa fiye da 41,595. Kazalika, ta kashe fiye da mutum 800 tun da ta ƙaddamar da hare-hare a Lebanon ranar 23 ga watan Satumba. Litinin, 30 ga watan Satumba, 2024 0822 GMT — Mutum fiye da 100,000 sun tsere daga Lebano...

A yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 360, ta kashe Falasɗinawa fiye da 41,595. Kazalika, ta kashe fiye da mutum 800 tun da ta ƙaddamar da hare-hare a Lebanon ranar 23 ga watan Satumba. Litinin, 30 ga watan Satumba, 2024 0822 GMT — Mutum fiye da 100,000 sun tsere daga Lebano...
