Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

KAI-TSAYE: Mutum 6,000 da suka samu munanan raunuka na bukatar 'kulawar gaggawa' a kasashen waje

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 94 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 22,835 sannan suka jikkata mutum 58,416, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 2300 GMT — Mutum 6,000 da suka samu munanan raunuka na bukatar 'kulawar gaggawa' a...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:13
KAI-TSAYE: Mutum 6,000 da suka samu munanan raunuka na bukatar 'kulawar gaggawa' a kasashen waje
Em resumo

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 94 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 22,835 sannan suka jikkata mutum 58,416, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 2300 GMT — Mutum 6,000 da suka samu munanan raunuka na bukatar 'kulawar gaggawa' a...

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 94 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 22,835 sannan suka jikkata mutum 58,416, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 2300 GMT — Mutum 6,000 da suka samu munanan raunuka na bukatar 'kulawar gaggawa' a kasashen waje Gwamnatin Gaza ta sanar cewa mutun 6,000 da suka samu munanan raunuka sakamakon hare-haen da Isra'ila take kai wa Gaza suna bukatar a fitar da su kasashen waje domin ba su kulawar gaggawa. A wata sanarwa da ofishin watsa labarai na Gaza ya fitar ya bayyana "babban bala'in" da fannin lafiya ya fada a cikin tun ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a yankin. Sanarwar ta ce asibitoci 30 a yankin sun daina aiki a yayin da aka jikkata fiye da mutum 58,000 sakamakon hare-hare. "Muna kira ga 'yan'uwanmu da ke Masar su yi gaggawar bude iyakar Rafah sannan su bari a fitar da mutum 6,000 daga Gaza wadanda suka samu munanan raunuka domin samun kulawar gaggawa saboda akwai karancin kayan aiki ga marasa lafiya a Gaza,” in ji sanarwar. 2100 GMT — Jirage marasa matuka na Isra'ila sun bude wuta a Asibitin Al Aqsa Martyrs — Ma'aikatar Lafiya Jirage marasa matuka na Isra'ila sun kai hare-hare a Asibitin Al Aqsa Martyrs da ke Tsakiyar Gaza, a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Lafiya ta yankin ta fitar. "Sojojin Isra'ila da ke mamaya sun yi amfani da jirage marasa matuka wurin kai hari kan marasa lafiya da ma'aikatan asibiti," in ji ma'aikatar ta lafiya. "Jiragen marasa matuka sun yi luguden wuta babu kakkautawa a kusa da gine-gine da yankunan da asibitin yake inda suke kai hari kan duk wani abu da suka ga yana motsi," sanarwar ta kara da cewa. Ta ce hare-haren sun jikkata marasa lafiya da sauran mutane inda ake tserewa daga asibitin yayin da jiragen ke bin mutane suna bude musu wuta. Yunkurin Isra'ila na ganin Asibitin Al Aqsa Martyrs ya daina aiki zai yi sanadin mutuwar dubban majinyata da ke cikinsa, in ji sanarwar. An kai mutanen da suka jikkata Asibitin Al Aqsa Martyrs bayan luguden wutar da Isra'ila ta yi a Deir Al Balah, Gaza ranar 7 ga watan Janairu, 2024. / Hoto: AA