Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Kai-tsaye: Mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza sun kai 34,388

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 204 tana yi a Gaza ya kashe 34,388 Falasɗinawa — kashi 70 daga cikinsu jarirai da ƙananan yara da mata — sannan mutum sama da 77,437 sun jikkata, yayin da ake fargabar mutum 8,400 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine. 0914 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza sun kai 34,388
Кратко

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 204 tana yi a Gaza ya kashe 34,388 Falasɗinawa — kashi 70 daga cikinsu jarirai da ƙananan yara da mata — sannan mutum sama da 77,437 sun jikkata, yayin da ake fargabar mutum 8,400 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine. 0914 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a...

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 204 tana yi a Gaza ya kashe 34,388 Falasɗinawa — kashi 70 daga cikinsu jarirai da ƙananan yara da mata — sannan mutum sama da 77,437 sun jikkata, yayin da ake fargabar mutum 8,400 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine. 0914 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza ya kai 34,388 Ma'aikatar kiwon lafiya ta Falasɗinu ta ce kawo yanzu adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a yankin ya kai 34,388. Mutanen da suka mutu sun haɗa da mutum 32 da dakarun Isra'ila suka kashe a awanni 24 da suka gabata, a cewar ma'aikatar kiwon lafiyar. Ta ƙara da cewa mutane 77,437 sun jikkata a Gaza tun da Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a yankin ranar 7 ga watan Oktoba. 0906 GMT — Mutum ɗaya ya mutu yayin da Isra'ila ta yi luguden wuta a wasu garuruwa na kudancin Lebanon Aƙalla mutum guda ya mutu a Lebanon yayin da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai hare-hare biyu a garuruwan Kafr Shuba da Shebaa da ke kudancin ƙasar. "Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai samame sau biyu da sanyin safiya a garuruwan Kafr Shuba da Shebaa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Qasim Asaad a garin Kafr Shuba da kuma rusa gidaje biyus," a cewar kamfanin dillancin labarai na Lebanon. Kawo yanzu Isra'ila ba ta ce komai game da wannan batu ba. 0043 GMT — Hamas ta ce tana nazari kan sabbin sharuɗɗan tsagaita wuta na Isrra'ila Ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas ta ce ta karbi bayanai daga Isra'ila game da sabbin sharuddan tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su kuma tana yin nazari a kansu. "A yau, ƙungiyar Hamas ta karɓi bayabai daga Yahudawa ƴan mamaya game da batun tsagaita, waɗanda masu shiga tsakanin daga Masar da Qatar suka gabatarranar 13 ga watan Afrilu," a cewar Khalil al Hayya, mataimakin shugaban ɓangaren siyasa na Hamas, a wata taƙaitacciyar sanarwa da ya fitar. "Ƙungiyarmu za ta yi nazari a kansu, kuma da zarar mun kammala za mu bayar da amsa." Khalil al Hayya, mataimakin shugaban ɓangaren siyasa na Hamas ya ce za su fitar da matsayarsu da zarar sun gama nazari kan bayanai da Isra'ila ta miƙa musu./Hoto: AFP