Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 86 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 21,672 tare da jikkata 56,165 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da ragargazar garuruwa da birane da sansanonn 'yan gudun hijira. 0115 —Mun kashe karin sojojin Isra'ila 20 tare da jikkata wasu a Gaza: Al Qassam Brigades Al Qassam Brigades, wanda shi ne bangaren sojoji na kungiyar Hamas, ya dakarunsa sun kashe sojojin Isra'ila sama da 20 tare da jikkata da dama a wani gumurzu da suka yi a Birnin Gaza. A wani sako da ya wallafa a manhajar Telegram, Al Qassam Brigades ya ce mayakansa sun yi arangama da dakaru na musamman na Isra'ila da ke “kutsawa yankin Sheikh Radwan da ke Birnin Gaza, lamarin da ya kai ga kisan sojoji fiye da 20 tare da jikkata wasu.” A wani sako na daban, bangaren sojin na Hamas ya ce mayakansa sun kai hari kan “tankar yakin Isra'ila ta Merkava da abubuwan fashewa na Sho'ath a yankin Sheikh Radwan na Gaza.” Kazalika mayakan Al Qassam Brigades sun yi amfani da makamai masu linzami suka ragargaji “wani gungun ababen hawa na Isra'ila da kuma sojojin kasar a birnin Khan Yunis na kudancin Zirin Gaza.”
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
KAI-TSAYE: Mun kashe karin sojojin Isra'ila 20 tare da jikkata wasu a Gaza: Al Qassam Brigades
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 86 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 21,672 tare da jikkata 56,165 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da ragargazar garuruwa da birane da sansanonn 'yan gudun hijira. 0115 —Mun kashe karin sojojin Isra'ila 20 tare da jikkata wasu a Gaza...

Em resumo