Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza - ya kwana na 75 - inda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 19,667, da jikkata wasu fiye da 52,586, yayin da ake fargabar dubban mutane sun mutu a karkashin baraguzan gine-ginen da aka kai wa hari. 0230 GMT — Mayakan Hamas sun gwabza da sojojin Isra'ila da suka mamaye titunan Gaza Mayakan gwagwarmayar Hamas da sojojin Isra'ila 'yan mamaya sun yi artabu da musayar wuta da bindigogi a kan titunan birnin na biyu mafi girma a Gaza, kamar yadda mazauna da kuma shaidu suka bayyana. Mazauna garin Khan Younis sun ba da rahoton ƙazamin faɗan bindigogi a yankunan tsakiya da gabashin birnin na kudancin kasar. Jami'an kiwon lafiya na Gaza sun ce an kashe Falasdinawa 12 a wani harin da Isra'ila ta kai kan wani gida a birnin. Isra'ila ta yi asarar sojoji 132 a fadan da ake a cikin Gaza tun bayan da ta mamaye yankin. Sabon faɗan na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta jinkirta kaɗa ƙuri'a kan yunƙurin ƙara kai kayan agaji ga yankin Falasdinu da ke fuskantar bala'in jinƙai. Hare-haren wuce gona da iri da Isra'ila ke yi, ya sa yankunan gaɓar tekun sun zama kango, tare da jawo yunwa da rashin matsuguni, ya kuma kashe Falasdinawa kusan 20,000, a cewar jami'an yankin. 2140 GMT — Shugaban Hamasa Haniyeh zai tafi Masar don tattaunawa kan kawo karshen yakin da Isra'ila ke yi a Gaza Ziyarar Haniyeh za ta kasance karo na biyu a Masar tun bayan fara yaƙin da Isra'ila ta yi a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba. Hoto: OTHERS Shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh na shirin kai ziyara kasar Masar domin tattaunawa kan batun tsagaita wuta a Gaza da kuma yarjejeniyar musayar fursunoni da Isra'ila, kamar yadda wata majiya da ke kusa da kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta bayyana. Majiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, Haniyeh wanda ke zaune a Qatar, zai jagoranci wata babbar tawaga ta Hamas zuwa Masar, inda zai tattauna da shugaban hukumar leƙen asirin Masar Abbas Kamel da ma wasu da daban. Tattaunawar za ta kasance "a kan dakatar da muguntar wuce gona da iri da yaƙi don shirya yarjejeniyar sakin fursunoni (da) kawo ƙarshen hare-haren da ake yi wa Gaza da aka yi wa ƙawanya", in ji majiyar, bisa sharaɗin sakaya sunansa, saboda ba shi da izinin yin magana game da ziyarar. A karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda a watan da ya gabata, Qatar ta taimaka wajen sasantawa, tare da samun goyon bayan Masar da Amurka, an sako Isra’ilawa 80 da aka yi garkuwa da su, a madadin Falasdinawa 240 da ke garƙame a gidajen yari na Isra’ila. Amma Isra'ila ta kama dubban Falasdinawa tun ranar 7 ga watan Oktoba. A cewar majiyar Hamas, tattaunawar da za a yi a Masar za ta mayar da hankali ne kan "isar da kayayyakin jinƙai, da janyewar sojojin Isra'ila daga Gaza da kuma mayar da 'yan gudun hijira zuwa garuruwa da ƙauyukan da ke arewacin kasar". Ziyarar Haniyeh za ta kasance karo na biyu a Masar tun bayan fara yaƙin da Isra'ila ta yi a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba, bayan wata ziyarar da ya kai a farkon watan Nuwamba. 2230 GMT — Kungiyar masu ikirarin jihadi sun saki bidiyo na wasu Isra'ilawa biyu da suke rokon a sake su Rundunar mayakan Al Quds ta Kungiyar Gwagwarmayar Falasdinawa tmasu ikirarin jihadi, Palestinian Islamic Jihad ta saki wani bidiyoa shafin Telegram na wasu Isra'ilawa maza biyu da ake garkuwa da su a Gaza suna rokon da a sake su. Mutanen biyu sun bayyana sunayensu da Gadi Moses da Elad Katsir kuma sun bayyana a wani dan gajeren faifan bidiyo suna neman a ƙara ƙaimi domin su sake haɗuwa da iyalansu. "Muna mutuwa a tsaitsaye. Muna cikin wani yanayi da ba za mu iya jurewa ba," in ji Moses, ya faɗa yana kallon kyamarar daga wani waje da ba a iya ganewa. Mutanen biyu duk ba su yi aski ba kuma da alama sun rame. Moses Bayahude ne ɗan kama wuri zauna kuma manomi mai kimanin shekaru 79 da aka kama shi daga Kibbutz a ranar 7 ga Oktoba lokacin da mayakan Hamas suka kai wani samame a kudancin Isra'ila. Katsir, mai shekaru 47, kuma an dauke shi daga Kibbutz tare da mahaifiyarsa, wanda daga baya aka sake shi. An kashe mahaifinsa, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
KAI-TSAYE: Mayakan Hamas sun gwabza da sojojin Isra'ila da suka mamaye titunan Gaza
Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza - ya kwana na 75 - inda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 19,667, da jikkata wasu fiye da 52,586, yayin da ake fargabar dubban mutane sun mutu a karkashin baraguzan gine-ginen da aka kai wa hari. 0230 GMT — Mayakan Hamas sun gwabza da sojojin Isra'ila d...

Em resumo
Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza - ya kwana na 75 - inda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 19,667, da jikkata wasu fiye da 52,586, yayin da ake fargabar dubban mutane sun mutu a karkashin baraguzan gine-ginen da aka kai wa hari. 0230 GMT — Mayakan Hamas sun gwabza da sojojin Isra'ila d...
