Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kai-tsaye: Matakin da Isra'ila ta ɗauka na rusa asibitoci a Gaza 'kisan kiyashi ne' — rahoto

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 452 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 45,541 da jikkata mutum fiye da 108,338. A Lebanon, Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 4,048 tun daga Oktoban 2023. Talata, 31 ga watan Disamba, 2024 2119 GMT — Matakin da Isra'ila ta ɗauka...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
Kai-tsaye: Matakin da Isra'ila ta ɗauka na rusa asibitoci a Gaza 'kisan kiyashi ne' — rahoto
A taƙaice

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 452 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 45,541 da jikkata mutum fiye da 108,338. A Lebanon, Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 4,048 tun daga Oktoban 2023. Talata, 31 ga watan Disamba, 2024 2119 GMT — Matakin da Isra'ila ta ɗauka...

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 452 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 45,541 da jikkata mutum fiye da 108,338. A Lebanon, Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 4,048 tun daga Oktoban 2023. Talata, 31 ga watan Disamba, 2024 2119 GMT — Matakin da Isra'ila ta ɗauka na rusa asibitocin da ke arewacin Gaza wani ɓangare ne na "kisan kiyashin" da take yi wa Falasɗinawa, kamar yadda jaridar Haaretz da ake wallafawa a Isra'ila ta bayyana a wani sharhi da ta buga. Jaridar ta soki sojojin Isra'ila kan irin zaluncin da suke aikatawa a arewacin Gaza, tana mai cewa suna yin hakan ne domin hana Falasɗinawa komawa gidajensu. Jaridar ta ce ruseh-rushen da Isra'ila take yi, musamman na asibitoci, suna tilasta wa mutane tserewa zuwa kudanci domin neman magunguna. Ta jaddada cewa bai kamata a bar yanki mai girma irin wannan ba tare da asibitoci ba, musamman a lokutan yaƙi, inda ta jawo hankali kan Yarjejeniya ta Huɗu ta Geneva wadda ta buƙaci a kare asibitoci a lokacin yaƙi. Ƙarin labarai???? 0134 GMT — Isra'ila ta ce ta kakkaɓo wani makami mai linzami da aka harba mata daga Yemen Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kakkaɓo wani makami mai linzami da mayaƙa Houthi suka harba mata daga Yemen, lamarin da ya sa aka riƙa kaɗa jiniya a yankunan tsakiyar ƙasar, ciki har da birnin Tel Aviv. 2023 GMT — An yi kutse a shafin X na kamfanin Ford, an wallafa saƙonnin goyon bayan Falasɗinawa Rahotanni sun bayyana cewa an yi kutse a shafin X na kamfanin ƙera motoci na Ford, sannan aka riƙa wallafa saƙonnin da ke goyon bayan Falasɗinawa. Saƙonnin da aka wallafa sun haɗa da "A Sakar wa Falasɗinawa Mara", "Isra'ila 'yar ta'adda ce," da kuma "HANKALIN KOWA YANA KAN GAZA."