Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Kai-tsaye: Masu shiga tsakani na matsa wa Isra'ila da Hamas lamba su cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga rana ta 240, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,379 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — ya kuma jikkata mutum 82,407, a cewar hukumomi. 2211 GMT — Masu shiga tsakani na Qatar da Masar da Amurka sun yi kira ga Isra'ila da Hamas su "ƙarƙare" cimm...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:13
Kai-tsaye: Masu shiga tsakani na matsa wa Isra'ila da Hamas lamba su cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta
Bu haberde ne var?

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga rana ta 240, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,379 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — ya kuma jikkata mutum 82,407, a cewar hukumomi. 2211 GMT — Masu shiga tsakani na Qatar da Masar da Amurka sun yi kira ga Isra'ila da Hamas su "ƙarƙare" cimm...

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga rana ta 240, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,379 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — ya kuma jikkata mutum 82,407, a cewar hukumomi. 2211 GMT — Masu shiga tsakani na Qatar da Masar da Amurka sun yi kira ga Isra'ila da Hamas su "ƙarƙare" cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Shugaban Amurka Joe Biden ya tsara, a daidai lokacin da dakaraun Isra'ila ke ƙara zafafa ruwan wuta a kudancin Gaza. To sai dai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tuni ya jaddada cewa ƙasarsa za ta ci gaba da yaƙi har sai yaƙin ya cimma manufarsa. Ya nanata wannan matsayi ne a ranar Asabar, yana mai cewa "sharuɗan da Isra'ila ta gindaya don kawo ƙarshen yaƙin ba su sauya ba: rusa Hamas ta fuskar soja da shugabanci, da kuɓutar da duka mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma tabbatar da cewa Gaza ba za ta sake zama barazana ga Isra'ila ba". Ita kuma ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa ta ce tana duban shirin na Isra'ila da Biden ya tsara da "kyakkyawan fata." A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa, Qatar da Amurka da Masar sun ce " a msatayinmu na masu shiga tsakani a tattaunawar da ake ci gaba da yi don tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da waɗanda ake tsare da su", sun yi "kira ga Hamas da Isra'ila su yi aiki da yarjejeniyar da daftarin Shugaban Joe Biden ta tsara". 2241 GMT — Dubban Isra’ilawa sun nemi a yi musayar fursunoni da ƙungiyoyin Falasaɗinawa Dubban Isra’ilawa sun yi zanga-zanga a Tel Aviv don neman a cimma yarjejeniyar musayar fursunoni da ƙungiyoyin Falasaɗinawa, sannan a gudanar da zaɓe da wuri, a cewar kafofin watsa labarai. Dubban ɗaruruwan mutanen ne suka shiga zanga-zangar a baban birnin ƙasar da ake yi duk mako a Dandalin Kaplan a tsakiyar Tel Aviv, suna neman a cimma yarjejenyar musayar fursunoni nan take, abin da zai kai ga sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza, kamar yadda jaridar Yedioth Ahronoth ta rawaito. Iyalen mutanen da aka yi garkuwa da su sun nemi Benjamin Netanyahu ya yi amfani da daftarin tsagaita wuta da Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar ranar Juma’a.