Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 270 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,900 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 87,060 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 0227 GMT — Jami'an lafiya da na gudanarwa sun fara kwashe marasa lafiya daga asibitin European Hospital da ke Gaza a birnin Khan Younis gabanin yiwuwar Isra'ila ta sake kai farmaki yankin. Jami'an na lafiya sun fara kwashe marasa lafiya da waɗanda suka ji rauni da kuma kayan aikin kula da lafiya saboda asibitin yana cikin yankin da mazaunansa suka samu saƙonnin Isra'ila tana ba su wa'adi da su fice zuwa wani wajen. Majiyoyin lafiya sun shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na Anadolu Agency cewa jami'an lafiya sun kwashe mutane da dama zuwa asibitin Naseer a tsakiyar Khan Younis. Sun ƙara da cewa su ma jami'an gudanarwar asibitin sun kwashe wasu kayan kula da lafiya saboda tsoron za a lalata su idan Isra'ila ta kai hari asibitin. Wani wakilin Anadolu ya ba da rahoton cewa su ma mutanen da yaƙi ya raba da gidajensu suna cire tantunansu a kusa da asibitin suna komawa wasu wuraren, bayan samun barazanar farmakin Isra'ila.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Kai-tsaye: Marasa lafiya na tserewa daga asibitin Khan Younis kafin Isra'ila ta sake afka masa
Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 270 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,900 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 87,060 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 0227 GMT — Jami'an lafiya da na gudanarwa sun fara k...

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 270 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,900 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 87,060 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 0227 GMT — Jami'an lafiya da na gudanarwa sun fara k...
