Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

KAI-TSAYE: 'Makaman roka da aka harba Isra'ila daga Gaza na daga cikin mafiya ƙarfi'

Tsawon kwanaki 102, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,100 da raunata mutum 60,834. 1016 GMT — 'Makaman roka da aka harba Isra'ila daga Gaza na daga cikin mafiya...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
KAI-TSAYE: 'Makaman roka da aka harba Isra'ila daga Gaza na daga cikin mafiya ƙarfi'
De un vistazo

Tsawon kwanaki 102, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,100 da raunata mutum 60,834. 1016 GMT — 'Makaman roka da aka harba Isra'ila daga Gaza na daga cikin mafiya...

Tsawon kwanaki 102, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,100 da raunata mutum 60,834. 1016 GMT — 'Makaman roka da aka harba Isra'ila daga Gaza na daga cikin mafiya ƙarfi' Isra'ila ta ce an harba makaman rokoki 15 zuwa kudancin Isra'ila, inda suka lalata wani shago. Kafar yaɗa labaran Isra'ila ta ce lamarin na daga cikin hare-hare mafi ƙarfi da aka kai daga Gaza a cikin fiye da mako ɗaya. Gidan talabijin na Channel 12 ya rawaito cewa an ƙaddamar da harba rokokin ne daga garin Bureij da ke tsakiyar Gaza. Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan da Ministan Tsaro Yoav Gallant ya ce rundunar sojin Isra'ila na faɗaɗa ƙrfin ikon sojinta a arewacin Gaza zuwa sauran yankunan da ke zirin. 1025 GMT — Adadin Falasdinawan da aka kashe a Gaza ya kai 24,285 Ma’aikatar Lafiya a Gaza da ke Falasdinu ta ce zuwa yanzu akalla mutum 24,285 Isra’ila ta kashe tun daga 7 ga watan Oktoba a Gaza. Ma’aikatar a wata sanarwa da ta fitar ta ce zuwa yanzu Isra’ilar ta raunata mutum 61,154 a Falasdinu baki daya. 0931 GMT — Isra'ila ta ce ta kai hari iyakar Lebanon domin 'kawar da barazana' Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa sojojinta na musamman sun kai hari yankunan Ayta ash Shab da ke Lebanon. “Dakarun IDF na musamman sun kai hari domin kawar da barazana daga yankin Ayta ash Shab da ke Lebanon,” kamar yadda sojoji suka bayyana. Haka kuma sojojin sun ce jirgin yakin su ya kai hari kan wata mota mai harba makami mai linzami a kudancin Lebanon mallakar kungiyar Hezbollah ta Iran.