الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: Majalisar Ɗinkin Duniya ta ba da bayanin mummunar tasirin yaƙin Isra'ila a birnin Gaza

Isra'ila ta kwashe kwana 277 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,193 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 87,903, kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai. 2119 GMT — Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce wa'adin baya-bayannan da Isra'ila ta bayar da...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: Majalisar Ɗinkin Duniya ta ba da bayanin mummunar tasirin yaƙin Isra'ila a birnin Gaza
لمحة سريعة

Isra'ila ta kwashe kwana 277 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,193 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 87,903, kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai. 2119 GMT — Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce wa'adin baya-bayannan da Isra'ila ta bayar da...

Isra'ila ta kwashe kwana 277 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,193 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 87,903, kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai. 2119 GMT — Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce wa'adin baya-bayannan da Isra'ila ta bayar da ya tilasata wa Falasɗinawa ficewa daga wani ɓangare na birnin Gaza da aka mamaye ya shafi fiye da makarantu 60 inda Falasɗinawan da yaƙi ya raba da gidajensu suke samun mafaka, tare da wasu abitoci biyu da suke aiki rabi-da-rabi da wuraren karɓar magani shida da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko guda biyu. Su ma jami'an ba da agaji sun ba da rahoton cewa ma'aikata da marasa lafiya sun tsere daga asibitoci a wuraren da Isra'ila ta yi wa barazana da ma kusa da su, kuma an sake tilasta wa mutanen da dama da suka bar gidajensu sake guduwa a yanzu, kamar yadda mai magana da yawun Majalisar Ɗinkin Duniya Stephane Dujarric ya bayyana. Ofishin na ba da agaji ya kuma ba da rahoton cewa luguden wuta, da lalata hanyoyi, da rashin iya zuwa wurare da rashin doka da oda na ci gaba da hana zirga-zirga a kan babbar hanyar kai agaji daga mashigar Kerem Shalom [Karam Abu Salem] zuwa Khan Younis, sannan zuwa Deir al-Balah," a cewar Dujarric. Ya ce hakan ya haifar da mummunan ƙarancin abinci, ya kuma rage abincin da ake rabawa a tsakiya da kudancin Gaza a watan jiya, da kuma ƙaruwar fargabar lalacewar kayan agajin, musasmman abinci saboda zafin rana. "A yanzu gidajen burodi uku daga 18 da abokan aikinmu masu agaji suke tallafawa ne kawai suke aiki a Gaza, dukkansu a Deir al-Balah," kamar yadda Dujarric ya bayyana. "Yayin da rashin makamashi ya tilasta wa gidajen burodin da suke aiki kaɗan suka dakatar da aiki baki ɗaya." Maysa Saleh, jami'in ilimi na ƙungiyar ba da agaji ta Norwegian Refugee Council a Deir al-Balah ya ce "kusan babu agajin da ya iso tun makon jiya ko makamancin haka," sannan "abinci shi ne babban abin da aka fi damuwa da shi."