Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, ya shiga rana ta 201. An kashe aƙalla Falasdinawa 34,183 - galibinsu jarirai da yara da mata. An raunata wasu sama da 77,143. MDD ta ce an aikata "laifin yaƙi" bayan gano gawa sama da 300 a kaburburan bai-ɗay 0200 GMT — Majalisar Dattawan Amurka ta ba da tallafin dala biliyan 26.6 ga Isra'ila Majalisar Dattawan Amurka ta amince a bai wa Isra’ila tallafin soji har na dala biliyan 26.6, ga ƙawar tata da ake zargi da yi wa Falasɗinawan da ke Gaza kisan ƙare dangi ta hanyar amfani da makaman Amurka. Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alkawarin sanya hannu cikin sauri kan ƙudurin na dala biliyan 61 - wanda ya hada da tallafi ga Ukraine da Taiwan - bayan da Majalisar ta ba da amincewarta ta karshe, yana mai cewa za a fara isar da tallafin da ake bukata a wannan makon. Amurka ta bayyana goyon bayanta ga Isra'ila tun farkon yaƙin a watan Oktoban bara. Amurka ba ta taɓa ja da baya ba wajen bai wa Isra'ila makamai, ba tare da la'akari da asarar rayukan fararen hula da ake yi a Gaza ba. Amurka tana bai wa Isra'ila dala biliyan 3.8 a matsayin tallafin soji na shekara-shekara kuma galibi tana bai wa ƙawayenta garkuwa a Majalisar Dinkin Duniya. 2145 GMT — Isra'ila na shirin mamaye Rafah nan ba da jimawa ba - rahoto Bayan yi watsi da roƙon da ƙasashen duniya suka yi wa Isra'ila da zargin kisan ƙare dangi da ake mata, sojojin Isra'ila na shirin mamaye birnin Rafah da ke kudancin Gaza "nan ba da jimawa ba," a cewar kafafen yada labaran Isra'ila. A cewar kafar watsa labaran Isra'ila ta KAN, wacce ta ambato wasu majiyoyin soji da ba ta bayyana sunansu ba, rundunar sojin na shirin kai hare-hare ta ƙasa a Rafah, ciki har da "kwashe wasu mazauna yankin masu yawa." "Bisa shirin da sojojin suka yi, za a bukaci Falasdinawa sama da miliyan daya da ke Rafah da su ƙaurace wa yankin zuwa matsugunan da aka kafa kwanan nan a yankunan kudanci da tsakiyar Zirin Gaza," a cewar kafar watsa labaran.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Kai-tsaye: Majalisar Dattawan Amurka ta amince da bai wa Isra'ila tallafin soji na dala biliyan 26.6
Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, ya shiga rana ta 201. An kashe aƙalla Falasdinawa 34,183 - galibinsu jarirai da yara da mata. An raunata wasu sama da 77,143. MDD ta ce an aikata "laifin yaƙi" bayan gano gawa sama da 300 a kaburburan bai-ɗay 0200 GMT — Majalisar Dattawan Amurka ta ba da tallafin d...

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, ya shiga rana ta 201. An kashe aƙalla Falasdinawa 34,183 - galibinsu jarirai da yara da mata. An raunata wasu sama da 77,143. MDD ta ce an aikata "laifin yaƙi" bayan gano gawa sama da 300 a kaburburan bai-ɗay 0200 GMT — Majalisar Dattawan Amurka ta ba da tallafin d...
