Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kai-tsaye: Lebaanon ta ce abin da Isra'ila ke yi na far wa dakarun MDD 'laifukan yaƙi ne'

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 399 — ya kashe akalla Falasdinawa 43,469 da jikkata 102,560, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,103 tun Oktoban bara. Friday, November 8, 2024 0116 GMT — Lebanon ta yi...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
Kai-tsaye: Lebaanon ta ce abin da Isra'ila ke yi na far wa dakarun MDD 'laifukan yaƙi ne'
A taƙaice

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 399 — ya kashe akalla Falasdinawa 43,469 da jikkata 102,560, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,103 tun Oktoban bara. Friday, November 8, 2024 0116 GMT — Lebanon ta yi...

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 399 — ya kashe akalla Falasdinawa 43,469 da jikkata 102,560, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,103 tun Oktoban bara. Friday, November 8, 2024 0116 GMT — Lebanon ta yi tur da harin jirgi marar matuƙi da Isra'ila ta kai birnin Sidon da ke kudancin ƙasar wanda ya kashe farar hula uku da kuma jikkata sojojin Lebanon da na Majalisar Dinkin Duniya da dama, tana mai ayyana hakan a matsayin "laifin yaƙi". Dakarun wanzar da zaman lafiya biyar sun jikkata a harin, wanda aka kai kusa da birnin Sidon na kudancin Lebanon, in ji MDD. Rundunar sojin Lebanon ta tabbatar da cewa an kai harin ne da wani jirgin Israi'la marar matuƙi a kan wata mota, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum uku da ke ciki tare da jkkata uku daga sojojinta a wani shingen bincike da ke kusa da wajen. Ministan Harkokin Wajen Lebanon ya ce ƙasar ta yi kakkausan Allah wadai da cin zalin na Isra'ila tare da yin kira ga ƙasashen duniya da su yi tur da irin wadannan hare-hare a kuma ɗora wa Isra'ila alhakin hakan. Ma'aikatar ta bayyana harin a matsayin "zafafa wa kan abin da Isra'ila ke yi na far wa dakarun wanzar da zaman lafiya na UNIFIL, da sojojin Isra'ila da fararen hula, kuma laifukan yaƙi ne da take dokokin jinƙai na ƙasashen duniya."