Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Kai-tsaye: Kwashe mutane da Isra'ila ke yi daga Rafah na iya jawo mummunan rikici — Hamas

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 213, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,683 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,018 ne suka jikkata. 0754 GMT — Kwashe mutane da Isra'ila ke yi daga Rafah na iya jawo mummunar ta'azzarar rikici...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Kwashe mutane da Isra'ila ke yi daga Rafah na iya jawo mummunan rikici — Hamas
Кратко

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 213, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,683 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,018 ne suka jikkata. 0754 GMT — Kwashe mutane da Isra'ila ke yi daga Rafah na iya jawo mummunar ta'azzarar rikici...

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 213, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,683 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,018 ne suka jikkata. 0754 GMT — Kwashe mutane da Isra'ila ke yi daga Rafah na iya jawo mummunar ta'azzarar rikicin — Hamas Babban jami'in Hamas Sami Abu Zuhri ya ce kwashe mutane da Isra'ila ke yi daga Rafah gabanin hare-haren da ake sa ran za ta ƙaddamar wani "mummunan lamari ne da ka iya ta'azzara yaƙin da ake yi, kuma zai jawo ɗumbin matsaloli." Kazalika jami'an Hamas sun yi ikirarin cewa matakin kwashe Falasdinawa daga Rafah zai jawo tsaiko wajen sasantarwar sakin mutanen da ake garkuwa da su. Sojojin Isra'ila sun fara kwashe mutane da ga yankunan da ke kusa da kan iyakar gabashin Rafah, gabain wani farmaki ta ƙasa da ake sa ran za a kai a birnin Falasɗinun da ke kudancin Gaza a yau. Duk da ƙaruwar adawa da yake fuskanta daga ƙasashen duniya, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin kai farmaki Rafah, yankin da ke ɗauke da Falasɗinawa fiye da miliyan 1.4 da ke neman mafaka a wajen. 0615 GMT — Hezbollah ta Labanon ta ce ta harba gomman rokoki a wani sansanin sojon Isra'ila Ƙungiyar Hezbollah ta Labanon da ke samun goyon bayan Iran ta ce ta harba gomman makaman rokokin Katyusha a wani sansanin sojin Isra'ila da ke Tuudan Golan da aka mamaye, a wani martani ga wani hari da Isra'ilan ta kai gabashin Labanon. Mayaƙan Hezbollah sun ƙaddamar da "gomman hare-haren makaman rokoki na Katyusha" da nufin samun hedikwatar sansanin soji da ke Tuddan Golan," kamar yadda ƙungiyar ta faɗa a wata sanarwa, tana mai cewa "harin martanin ne kan harin da maƙiya suka kai yankin Bekaa."