Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Kai-tsaye: Kwamitin Tsaro na MDD ya yi taron gaggawa bayan Isra'ila ta yi kisan kiyashi a Rafah

Isra'ila ta kwashe fiye da wata shida na kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 36,050 — cikinsu har da jarirai da yara da mata —sannan ta jikkata sama da mutum 81,026, kana. 2126 GMT — Kwamitin Tsaro na MDD ya yi taron gaggawa bayan Isra'ila ta yi kisan kiyashi a Rafah Kwamitin Ts...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Kwamitin Tsaro na MDD ya yi taron gaggawa bayan Isra'ila ta yi kisan kiyashi a Rafah
Kwa muhtasari

Isra'ila ta kwashe fiye da wata shida na kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 36,050 — cikinsu har da jarirai da yara da mata —sannan ta jikkata sama da mutum 81,026, kana. 2126 GMT — Kwamitin Tsaro na MDD ya yi taron gaggawa bayan Isra'ila ta yi kisan kiyashi a Rafah Kwamitin Ts...

Isra'ila ta kwashe fiye da wata shida na kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 36,050 — cikinsu har da jarirai da yara da mata —sannan ta jikkata sama da mutum 81,026, kana. 2126 GMT — Kwamitin Tsaro na MDD ya yi taron gaggawa bayan Isra'ila ta yi kisan kiyashi a Rafah Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya gudanar da taron gaggawa bayan wani hari da gangan da Isra'ila ta kai sansanin Falasɗinawa 'yan gudun hijira a birni Rafah da ke kudancin Gaza, lamarin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 45 kana ya jikkata fiye da mutum 250. Wasu daga cikin mutanen an kashe su ne ta hanya yin gunduwa-gunduwa da su, yayin da aka ƙona wasu. Ƙasar Aljeriya ce ta buƙaci a yi taron gaggawar, ko da yake ita wakiliyar dindindin ba ce ta majalisar. 2017 GMT — Sakatare Janar na MDD ya soki Isra'ila kan harin da ta kai Rafah Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tir da Isra'ila kan harin da ta kai yankin Rafah da ke kudancin Gaza, yana mai cewa harin ya yi sanadin "mutuwar fararen-hula da ba su da laifi waɗanda ke samun mafaka daga munanan hare-haren da ake kai wa." "Babu wani tudun-mun-tsira a Gaza. Dole a daina wannan bala'i," in ji Guterres a saƙon da ya wallafa a soshiyal midiya.