Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

KAI-TSAYE: Kusan kashi hudu na al'ummar Gaza sun mutu, sun ji rauni ko sun bace - Kungiyar Euro-Med

Luguden wutar da Isra'ila ta kwashe kwana 92 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 22,600 tare da jikkata 59,910 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da ragargazar garuruwa da birane da sansanonn 'yan gudun hijira. 1040 GMT — Kusan kashi hudu na al'ummar Gaza sun mutu, sun ji rauni ko...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:13
KAI-TSAYE: Kusan kashi hudu na al'ummar Gaza sun mutu, sun ji rauni ko sun bace - Kungiyar Euro-Med
Bu haberde ne var?

Luguden wutar da Isra'ila ta kwashe kwana 92 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 22,600 tare da jikkata 59,910 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da ragargazar garuruwa da birane da sansanonn 'yan gudun hijira. 1040 GMT — Kusan kashi hudu na al'ummar Gaza sun mutu, sun ji rauni ko...

Luguden wutar da Isra'ila ta kwashe kwana 92 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 22,600 tare da jikkata 59,910 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da ragargazar garuruwa da birane da sansanonn 'yan gudun hijira. 1040 GMT — Kusan kashi hudu na al'ummar Gaza sun mutu, sun ji rauni ko sun bace - Kungiyar Euro-Med Sama da mutum 90,000, wato kusan kashi 4 cikin 100 na al’ummar Gaza a halin yanzu ko dai sun mutu ko sun samu rauni ko sun bace, kamar yadda wata kungiyar kare hakkin bil adama ta bayyana Kungiyar Euro-Mediterranean Human Rights Monitor ta bayyana haka ne bayan binciken da ta yi dangane da irin hare-haren ta sama da kasa da ruwa da ke ci gaba da kaiwa a Gaza wadanda suka lalata kaso 70 cikin 100 na ababen more rayuwa a birnin. Kungiyar ta zargi Isra'ila da mayar da Zirin Gaza wurin da ba zaman lafiya. Daruruwan gawarwakin da ba za a iya daukarsu ba sun kasance a kan tituna, a cewar kungiyar, musamman a yankunan da sojojin Isra'ila suka kai farmaki ta kasa.