Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

KAI-TSAYE: Kungiyar Hezbollah ta ce ta kakkabo jirgin Isra'ila maras matuki

Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0850 GMT — Kungiyar Hezbollah ta ce ta kakkabo jirgin Isra'ila maras matuki Ku...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:13
KAI-TSAYE: Kungiyar Hezbollah ta ce ta kakkabo jirgin Isra'ila maras matuki
Em resumo

Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0850 GMT — Kungiyar Hezbollah ta ce ta kakkabo jirgin Isra'ila maras matuki Ku...

Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0850 GMT — Kungiyar Hezbollah ta ce ta kakkabo jirgin Isra'ila maras matuki Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta ce ta kakkabo jirgin Isra’ila maras matuki da makami mai linzami a yankin Galilee Panhandle. Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar da safe inda ta ce ta harba makamin nata da misalin karfe 1:45 agogon kasar, (23:45 agogon GMT). Ta bayyana cewa ta hango a lokacin da tarwatsatsun sassan jirgin ke faduwa ta yankin na Galilee Panhandle. Har yanzu Isra’ila ba ta fitar da sanarwa domin gasgatawa ko kuma karyata ikirarin na Hezbollah ba. Sama da Falasdinawa 12,000 Isra’ila ta kashe zuwa yanzu, inda sama da 8,300 yara ne da mata, haka kuma ta raunata sama da 30,000.