الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: Khamenei na Iran ya ce harin da Iran ta kai Isra'ila halal ne kuma mai inganci

Yakin kisan kare dangi na Isra'ila na kwanaki 364 a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 41,788. Hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon kuwa tun daga Oktoban shekarar 2023 ya yi sanadin mutuwar mutum 1,974 tare da watsa mutum miliyan 1.2. Juma'a 4 ga Oktoban 2024 0952 GMT –– Jagoran juyin juya...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: Khamenei na Iran ya ce harin da Iran ta kai Isra'ila halal ne kuma mai inganci
لمحة سريعة

Yakin kisan kare dangi na Isra'ila na kwanaki 364 a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 41,788. Hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon kuwa tun daga Oktoban shekarar 2023 ya yi sanadin mutuwar mutum 1,974 tare da watsa mutum miliyan 1.2. Juma'a 4 ga Oktoban 2024 0952 GMT –– Jagoran juyin juya...

Yakin kisan kare dangi na Isra'ila na kwanaki 364 a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 41,788. Hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon kuwa tun daga Oktoban shekarar 2023 ya yi sanadin mutuwar mutum 1,974 tare da watsa mutum miliyan 1.2. Juma'a 4 ga Oktoban 2024 0952 GMT –– Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ali Khamenei ya ce harin makami mai linzami na baya-bayan nan da Iran ta kai kan Isra'ila "shiri ne kuma halal ne" kuma shi ne mafi karancin hukuncin "laifi" na Isra'ila. A cikin jawabinsa na mintuna 40 ga dubban jama'a a Masallacin Mosalla, babban wurin addu'a a birnin Tehran, Khamenei ya ce harin da Hamas ta kai kusan shekara guda da ta gabata a ranar 7 ga Oktoba, 2023, matakin da al'ummar Falasdinu suka dauka ne. Ya kuma ce Iran ba za ta yi jinkiri ba kuma ba za ta yi gaggawar aiwatar da aikinta na tunkarar Isra'ila ba, ya kara da cewa harin makami mai linzami da aka kai kan Isra'ila yana bisa doka. Iran ta harba makami mai linzami kan Isra'ila a ranar Talata a wani matakin da ta ce na ramuwar gayya ne kan harin da Isra'ila ta kai a Beirut da ta kashe shugaban Hizbullah Nasrallah a ranar Juma'ar da ta gabata da kuma kisan gillar da aka yi wa shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Tehran a watan Yuli. 2100 GMT — Amurka ta goyi bayan mamayar Isra'ila a Lebanon yayin da ake ci gaba da kai hare-hare Beirut Gwamnatin Biden ta yi imanin cewa ya dace Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare ta kasa da ta sama kan kasar Lebanon a halin yanzu, in ji kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Matthew Miller, duk da cewa ya amince da hatsarin mamaye Lebanon din ya zarce manufofin Isra'ila a halin yanzu. Isra'ila ta aike da dakaru zuwa kudancin Lebanon a wannan makon bayan wani ƙazamin hari ta sama da aka kai tsawon makwanni biyu a cikin wani mummunan rikici da ya janyo Iran da kuma hadarin saka Amurka. Da yake magana a wani taron manema labarai a jiya Alhamis, Miller ya ce yanayin duk rikice-rikicen, ba za a iya tantance shi ba, don haka ba zai yiwu a fadi tsawon lokacin da Isra'ila za ta dauka ba wajen cimma burin da ta bayyana na kawar da ababen more rayuwa na Hezbollah a kudancin Lebanon, tare da ba da dama domin mayar da ‘yan Isra’ila da aka kora daga gidajensu da ke kan iyaka ta hanyar harba rokoki tsawonawatanni. 2130 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 37 a Lebanon cikin sa'o'i 24 Sanarwar da Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta fitar ta ce Isra'ila ta kashe akalla mutum 37 tare da jikkata wasu 151 a hare-haren da ta kai a fadin kasar Lebanon cikin sa'o'i 24 da suka gabata. A halin da ake ciki kuma, makami mai linzamin na Isra'ila ya kai hari a gefen filin jirgin saman Beirut, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito. Har ila yau Isra'ila ta kai hare-hare a yankunan kudancin Beirut "sau 11 a jere", in ji kamfanin dilancin labaran AFP, yana mai cewa an ji ƙarar jiniya kuma gine-gine sun girgiza a babban birnin Lebanon.