Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 271 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,925 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 87,141 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 2240 GMT — Babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce yunƙurin hanzartawa da daidaita aikin kai kayan agaji zuwa faɗin Falasɗinu ya samu "tasgaron ƙalubale", kuma kai kayayyakin ya yi "ƙasa sosai" tun da Isra'ila ta ƙaddamar da harin soji a kudancin birnin Rafah ranar 6 ga Mayu. Sama da al'ummar Gaza miliyan 1.9 daga cikin miliyan 2.3 sun tagayyara, kamar yadda Sigrid Kaag ta faɗa wa Kwamitin Tsaro na MDD. Ta ce harkar lafiya ta ruguje, an rusa makarantu, kuma zafin yanayi yana ƙaruwa, ga kuma ƙarancin ruwan sha da tsaftar muhalli, “haɗarin ɓarkewar cututtuka masu yaɗuwa yana ƙaruwa.” “Babu wani zaɓi ban da na aniyar siyasa, da cikakken girmama dokokin kare ɗan-adam, musamman kare farar hula, da samar da kyakkyawan yanayi don rarraba kayan agaji,” cewar Kaag, babbar jami'ar MDD kan agaji da sake gina Gaza. 0330 GMT — Isra'ila ta kashe gomman Falasɗinawa a hare-haren da ta kai Zirin Gaza Isra’ila ta kai wasu sabbin jeri hare-hare a Birnin Gaza, inda ta kashe gomman Falasɗinawa fararen hula, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinawa WAFA ya bayyana, inda yace an samu rahotannin jikkata mutane daga yankunan Sheikh Radwan da Shujaeya da kuma gabashin Birnin Gaza. Tun da farko, Isra’il ta kashe aƙalla fararen hula 12, ta kuma jikkata wasu a hare-haren jiragen sama a Deir al Balah a tsakiyar Gaza da aka mamaye, kamar yadda WAFA ya rawaito. Wakilin WAFA ya ce an kai gawawwakin mutane 12 Asibitin Shahidai na Al-Aqsa a Deir al Balah bayan hare-haren sama kan gidan iyalen Eslayyim a birnin. Isra’ila ta kuma kashen wasu fararen hular uku a yankin Al-Mansura a unguwar Shejaiya, da wasu ukun kuma daban a yammacin Rafah, a cewar kamfanin dillnacin labaran. Hukumomin lafiya sun shaida wa WAFA cewa daga wayewar gari an kai aƙalla gawawwakin fararen hula 31 asibitocin yankin.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Kai-tsaye: Kai kayan agaji zuwa Gaza ya yi 'ƙasa sosai' — MDD
Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 271 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,925 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 87,141 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 2240 GMT — Babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya ya...

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 271 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,925 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 87,141 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 2240 GMT — Babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya ya...
