Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kai-tsaye: Jordan za ta ƙarɓi baƙuncin taron gaggawa kan agaji ga Gaza

Yaƙin Isra’ila a Zirin Gaza da aka mamaye ya shiga rana ta 249, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 37,124 — kaso 71 mata da yara da jarirai — ya jikkata mutane 84,712, sannan an yi amanna fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka ruguza. 0208 GMT — Jordan za ta ƙarɓi baƙuncin wani taro...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
Kai-tsaye: Jordan za ta ƙarɓi baƙuncin taron gaggawa kan agaji ga Gaza
De un vistazo

Yaƙin Isra’ila a Zirin Gaza da aka mamaye ya shiga rana ta 249, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 37,124 — kaso 71 mata da yara da jarirai — ya jikkata mutane 84,712, sannan an yi amanna fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka ruguza. 0208 GMT — Jordan za ta ƙarɓi baƙuncin wani taro...

Yaƙin Isra’ila a Zirin Gaza da aka mamaye ya shiga rana ta 249, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 37,124 — kaso 71 mata da yara da jarirai — ya jikkata mutane 84,712, sannan an yi amanna fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka ruguza. 0208 GMT — Jordan za ta ƙarɓi baƙuncin wani taro kan buƙatar agajin gaggawa sakamakon hare-haren da Isra'ila ta shafe wata takwas tana kai wa Falasɗinawa a Gaza da aka mamaye, inda Isra'ila take yi wa mutane azaba da yunwa take kuma kashe waɗanda babu ruwansu. Taron yana fatan tattaro shugabannin duniya da shugabannin hukumomin ba da agaji don "tantance hanyoyin da za a haɓaka yadda ƙasashen duniya suke ɗaukar mataki kan mummunan yanayin da jama'a suke ciki a Zirin Gaza," kamar yadda hukumoin Jordan suka bayyana. Taron, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya da Jordan da Masar suka yi haɗin gwiwa wajen shirya gudanar da shi a gaɓar Tekun Bahar Mayyit, zai samu halartar Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken da Shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas. Ma'aikatar Harkokin Wajen Jordan ta ce taron zai tattauna "shirye-shiryen farfaɗo da Gaza na farko-farko, zai kuma nemi a yi alƙawura kan yin aiki tare bisa tsari don tunkarar mummunan yanayin da jama'a suke ciki a Gaza". "Babbar manufar wannan taron shi ne cim ma matsaya kan matakan da za a ɗauka don kula da buƙatun da ake da su na yanzu-yanzu" a Gaza, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa.