Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 162 tana kai wa Falasɗinawan da ke Gaza sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 31,490 tare da jikkata mutum fiye da 73,439 a yayin da Netanyahu ya amince da shirin mamaye Rafah duk da Allah wadai da duniya ke yi. 0115 GMT — Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe mata masu ciki da ƙananan yara 36 a sabbin hare-haren da suka kai Gaza Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hare-hare a sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, inda suka kashe Falasɗinawa fararen-hula aƙalla 36, gaibinsu ƙananan yara da mata masu ciki, a cewar wata sanar da hukumomn Falasɗinu suka fitar. "Sojojin mamaya na Isra'ila sun kai harin bama-bamai a gidan iyalan al Tabatibi da ke yammacin sansanin ƴan gudun hijira na al Jadid a Nuseirat (a tsakiyar Zirin Gaza), inda suka kashe Falasɗinawa 36, galibinsu ƙananan yara da mata masu ciki," in ji sanarwar. Sojojin sun kai hari kan gidaje aƙalla 12 na fararen-hula a Gaza, a cewar sanarwar. Ta ƙara da cewa, "Muna ɗora alhakin ƙaruwar kisan ƙare-dangi da ake yi wa fararen-hula kan gwamnatin Amurka, da manyan ƙasashen duniya da Isra'ila the international. Su ne kanwa uwar gami na waɗannan laifukan yaƙi da ake aikatawa."
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Kai-tsaye: Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe mata masu ciki da ƙananan yara 36 a sabbin hare-haren da suka kai Gaza
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 162 tana kai wa Falasɗinawan da ke Gaza sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 31,490 tare da jikkata mutum fiye da 73,439 a yayin da Netanyahu ya amince da shirin mamaye Rafah duk da Allah wadai da duniya ke yi. 0115 GMT — Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe mata...

Bu haberde ne var?
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 162 tana kai wa Falasɗinawan da ke Gaza sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 31,490 tare da jikkata mutum fiye da 73,439 a yayin da Netanyahu ya amince da shirin mamaye Rafah duk da Allah wadai da duniya ke yi. 0115 GMT — Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe mata...
