Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 93 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 22,835 sannan suka jikkata mutum 58,416, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 2100 GMT — Jirage marasa matuka na Isra'ila sun bude wuta a Asibitin Al Aqsa Martyrs — Ma'aikatar Lafiya Jirage marasa matuka na Isra'ila sun kai hare-hare a Asibitin Al Aqsa Martyrs da ke Tsakiyar Gaza, a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Lafiya ta yankin ta fitar. "Sojojin Isra'ila da ke mamaya sun yi amfani da jirage marasa matuka wurin kai hari kan marasa lafiya da ma'aikatan asibiti," in ji ma'aikatar ta lafiya. "Jiragen marasa matuka sun yi luguden wuta babu kakkautawa a kusa da gine-gine da yankunan da asibitin yake inda suke kai hari kan duk wani abu da suka ka yana motsi," sanarwar ta kara da cewa. Ta ce hare-haren sun jikkata marasa lafiya da sauran mutane inda ake tsrewa daga asibitin yayin da jiragen ke bin mutane suna bude musu wuta.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
KAI-TSAYE: Jirage marasa matuka na Isra'ila sun bude wuta a Asibitin Al Aqsa Martyrs — Ma'aikatar Lafiya
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 93 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 22,835 sannan suka jikkata mutum 58,416, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 2100 GMT — Jirage marasa matuka na Isra'ila sun bude wuta a Asibitin Al Aqsa Marty...