الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: Japan za ta yi aiki tare da Falasdinawa don tsagaita wuta a Gaza

Yakin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 333, akalla Falasdinawa 40,786 aka kashe kawo yanzu- akasarinsu mata da ƙananan yara, sannan fiye da mutane 94,22 ne suka jikkata, mutane 10,000 aka yi imanin suna binne a karkashin baraguzan gine-gine. Ranar Talata, 3 ga Satumba, 2024 1021 G MT — Japan za t...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: Japan za ta yi aiki tare da Falasdinawa don tsagaita wuta a Gaza
لمحة سريعة

Yakin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 333, akalla Falasdinawa 40,786 aka kashe kawo yanzu- akasarinsu mata da ƙananan yara, sannan fiye da mutane 94,22 ne suka jikkata, mutane 10,000 aka yi imanin suna binne a karkashin baraguzan gine-gine. Ranar Talata, 3 ga Satumba, 2024 1021 G MT — Japan za t...

Yakin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 333, akalla Falasdinawa 40,786 aka kashe kawo yanzu- akasarinsu mata da ƙananan yara, sannan fiye da mutane 94,22 ne suka jikkata, mutane 10,000 aka yi imanin suna binne a karkashin baraguzan gine-gine. Ranar Talata, 3 ga Satumba, 2024 1021 G MT — Japan za ta yi aiki tare da Falasdinawa don tsagaita wuta a Gaza Japan ta ce za ta yi aiki kafada da kafada da Falasdinawa domin cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare. Yayin wata ganawa da shugaban kwamitin Olympics na Falasdinu Jibril Rajoub a birnin Tokyo, Ministan Harkokin Wajen ƙasar Yoko Kamikawa ya bayyana "damuwa sosai" kan halin jinƙai a Gaza. Ta sake jaddada aniyar kasar Japan na tallafa wa kokarin samar da zaman lafiya da taimakon jinƙai, a cewar wata sanarwa a hukumance. Ta ƙara da cewa Tokyo na da niyyar "yin aiki kafada da kafada da bangaren Falasdinu don tsagaita wuta," in ji ta. Ƙarfe 06: 47 GMT - Hare-hare ta sama da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa a faɗin Gaza ya yi sanadiyar kashe Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu. Kamfanin dillancin labaran kasar Falasdinu Wafa ya ce an kashe Falasdinawa biyu tare da jikkata wasu a wani harin da Isra'ila ta kai kan wani sansani a arewa maso yammacin Khan Younis da ke kudancin Gaza. A sansanin 'yan gudun hijira na Bureij da ke tsakiyar Gaza jiragen yakin Isra'ila sun kai farmaki kan wani gida, yayin da motocin sojin Isra'ila suka yi luguden wuta kan sansanin lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka. 0625 GMT — An yi wa yara kusan 159,000 allurar rigakafin cutar shan inna a Gaza: Ma'aikatar Lafiya Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta sanar da cewa kusan yara 159,000 ne ake yi wa allurar rigakafin cutar shan inna a yankin tsakiyar Gaza. "Tawagogin lafiya sun samu damar yi wa yara 158,992 rigakafin a cikin kwana biyu tun bayan fara ta a Gaza," kamar yadda Ma'aikatar lafiyar ta faɗa a wata sanarwar. Ta ƙara da cewa 'yan ƙasar sun fita sosai don kai yaransu a yi musu allurar rigakafin a rana ta biyu da farawa. 0215 GMT — Biden ya yi amanna Netanyahu ba ya yin abin da ya dace don cim ma yarjejeniyar sakin fursunoni Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ba ya tunanin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yana yin abin da ya dace wajen kulla yarjejeniya da kungiyar Hamas kan sakin mutanen da ake garkuwa da su. Kalaman nasa na zuwa a matsayin martani ga tambayar da wani ɗan jarida ya yi masa a yayin da ya isa Fadar White House. Biden also said he believes a final deal for the release of hostages held by the Palestinian group is "very close." Biden ya kuma ce ya yi imanin an kusa cim ma yarjejeniyar karshe ta sakin mutanen da kungiyar Falasdinawan ta yi garkuwa da su."