Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kai-tsaye: Isra'ilawa sun yi cuncunrundo a kusa da ofishin Netanyahu, suna nema a cimma matsaya kan mutanen da aka yi garkuwa da su

Isra'ila ta kwashe kwana 230 tana kai hare-hare a Gaza abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 35,709 — galibinsu jarirai da mata da yara — sannan ta jikkata sama da mutum 79,990, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0125 GMT — Ɗaruruwan Isra'ilawa sun yi zanga-zanga...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ilawa sun yi cuncunrundo a kusa da ofishin Netanyahu, suna nema a cimma matsaya kan mutanen da aka yi garkuwa da su
A taƙaice

Isra'ila ta kwashe kwana 230 tana kai hare-hare a Gaza abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 35,709 — galibinsu jarirai da mata da yara — sannan ta jikkata sama da mutum 79,990, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0125 GMT — Ɗaruruwan Isra'ilawa sun yi zanga-zanga...

Isra'ila ta kwashe kwana 230 tana kai hare-hare a Gaza abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 35,709 — galibinsu jarirai da mata da yara — sannan ta jikkata sama da mutum 79,990, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0125 GMT — Ɗaruruwan Isra'ilawa sun yi zanga-zanga a ƙofar ofishin Firmaninstan Israi'ila Benjamin Netanyahu lokacin taron majalisar ministoci ta yaƙi, suna neman a sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza. Zanga-zanga ta kuma ɓarke a biranen Isra'ila da dama bayan an wallafa wani bidiyo da ke nuna mayaƙan Hamas sun kama wata sojan Isra'ila a wani sansanin sojoji da ke matsugunnin Yahudawa na Nahl OZ a kusa da katangar Gaza a ranar 7 ga Oktoban bara. A cikin wata sanarwa, Hamas ta ce "an jirkita bidiyon wanda ake yaɗawa a kafofin watsa labaran Isra'ila sannan ba ma za a iya tabbatar da sahihancinsa ba." Ta ƙara da cewa "yaɗa bidiyon na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta gaza ɓata sunan jajircewarmu ta hanyar yaɗa labaran da aka ƙirƙira da aka tabbatar da cewa na ƙarya ne, ta hanyar kafofin watsa labarai da dama da kuma bincikin da kafofin watsa labarai suka dinga yi." Wata jaridar Isara'ila Haaretz ta rawaito cewa mambobin majalisar yaƙin Benny Gantz da Gadi Eizenk da Ministan Tsaro Yoav Gallant sun gana da iyalen mutanen da aka yi garkuwa da su kafin a fara taron, amma Netanyahu bai ba da amsa ba ga buƙatar mutanen na gana wa da shi.