Isra'ila ta kwashe kwana 230 tana kai hare-hare a Gaza abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 35,709 — galibinsu jarirai da mata da yara — sannan ta jikkata sama da mutum 79,990, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0125 GMT — Isra'ilawa sun yi zanga-zanga a kusa da ofishin Netanyahu Ɗaruruwan Isra'ilawa sun yi zanga-zanga a ƙofar ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu lokacin taron majalisar ministoci ta yaƙi, suna neman a sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza. Zanga-zanga ta kuma ɓarke a biranen Isra'ila da dama bayan an wallafa wani bidiyo da ke nuna mayaƙan Hamas sun kama wata sojan Isra'ila a wani sansanin sojoji da ke matsugunin Yahudawa na Nahl OZ a kusa da katangar Gaza a ranar 7 ga Oktoban bara. A cikin wata sanarwa, Hamas ta ce "an jirkita bidiyon wanda ake yaɗawa a kafofin watsa labaran Isra'ila sannan ba ma za a iya tabbatar da sahihancinsa ba." Ta ƙara da cewa "yaɗa bidiyon na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta gaza ɓata sunanmu ta hanyar yaɗa labaran da aka ƙirƙira da aka tabbatar da cewa na ƙarya ne, ta hanyar kafofin watsa labarai da dama da kuma bincikin da kafofin watsa labarai suka dinga yi." Wata jaridar Isara'ila Haaretz ta rawaito cewa mambobin majalisar yaƙin Benny Gantz da Gadi Eizenk da Ministan Tsaro Yoav Gallant sun gana da iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su kafin a fara taron, amma Netanyahu bai ba da amsa ba ga buƙatar mutanen ta ganawa da shi.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Kai-tsaye: Isra'ilawa sun yi cincinrindo a kusa da ofishin Netanyahu, suna nema a cim ma matsaya kan mutanen da aka yi garkuwa da su
Isra'ila ta kwashe kwana 230 tana kai hare-hare a Gaza abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 35,709 — galibinsu jarirai da mata da yara — sannan ta jikkata sama da mutum 79,990, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0125 GMT — Isra'ilawa sun yi zanga-zanga a kusa da...

At a glance
Isra'ila ta kwashe kwana 230 tana kai hare-hare a Gaza abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 35,709 — galibinsu jarirai da mata da yara — sannan ta jikkata sama da mutum 79,990, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0125 GMT — Isra'ilawa sun yi zanga-zanga a kusa da...
