Tsawon kwanaki 111, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,700 da raunata mutum 63,740. 1123 GMT — An yi wa mutum 20 kisan kiyashi a mahadar kasar Kuwait a Gaza — Ma'aikatar Lafiya Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta ba da rahoton cewa Isra'ila ta yi wa mutum 20 kisan kiyashi, yayin da wasu 150 suka jikkata a mahaɗar Kuwait da ke Zirin Gaza, a lokacin da Falasdinawan da ke fama da yunwa ke jiran a kai musu agajin jinƙai. 1057 GMT — Yawan mutanen da suka mutu a gobarar tankar da ta tashi a kan gidajen marasa galihu na MDD a Gaza sun kai 12 — MDD Adadin wadanda suka mutu sakamakon gobarar tankar da ta tashi a sansanin Majalisar Dinkin Duniya a babban birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza ya karu zuwa 12, kamar yadda wani babban jami'in agaji na MDD ya sanar. "Yanzu an tabbatar da mutuwar mutum 12 tare da jikkata sama da 75, 15 daga cikinsu na cikin mawuyacin hali," in ji Thomas White, daraktan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Gaza ta UNRWA. A ranar Laraba ne wasu tankokin yaƙi biyu suka kai hari a sansanin Majalisar Dinkin Duniya inda dubban Falasɗinawa ke samun mafaka, in ji shi. Shugaban hukumar ta UNRWA Philippe Lazzarini ya ce harin bama-baman “rashin kula da muhimman ka’idojin yaƙi ne”. 0821 GMT — Hare-haren sama na Isra'ila sun kashe aƙalla Falasɗinawa 50 a Khan Younis cikin awa 24 Hamas tana neman Israi'la ta kawo ƙarshen munanan hare-haren da take kaiwa Gaza idan har tana so a cimma wata yarjejeniyar musayar fursunoni. / Photo: AFP Aƙalla Falasɗinawa 50 aka kashe a Khan Younis a cikin awa 24 da suka wuce, kamar yadda mai magana da yawun Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ya shaida wa Reuters. 0704 GMT — Qatar ta shaida wa Isra'ila cewa kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta dakatar da tattaunawar yarjejeniyar musayar fursunoni, a cewar kafar watsa labaran Isra'ila. "Hamas ta shaida wa masu shiga tsakani na Qatar cewa tana son sai Isra'ila ta janye baki ɗayan dakarunta daga Gaza tare da kawo ƙarshen yaƙin a matsayin mataki na farko kafin duk wata musayar fursunoni," kamar yadda kafar watsa labaran KAN ta Isra'ila ta ambato wata majiya da ta san komai game da batun take cewa. Sai dai har yanzu Qatar ba ta ce komai ba dangane da rahoton. An yi amannar cewa Hamas na tsare da Isra'ilawa 136 sakamakon hare-haren ba-zata da ta kai Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023. Hamas tana neman Israi'la ta kawo ƙarshen munanan hare-haren da take kaiwa Gaza idan har tana so a cimma wata yarjejeniyar musayar fursunoni. Gwamnatin Isra'ila ta yi watsi da kiraye-kirayen dakatar da yaƙin Gaza har sai an sakar mata fursunoninta sannan ta gama lalata Hamas.
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
KAI-TSAYE: Isra'ila ta yi wa Falasdinwa 20 kisan kiyashi a mahadar kasar Kuwait a Gaza — Ma'aikatar Lafiya
Tsawon kwanaki 111, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,700 da raunata mutum 63,740. 1123 GMT — An yi wa mutum 20 kisan kiyashi a mahadar kasar Kuwait a Gaza — Ma...

Em resumo
Tsawon kwanaki 111, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,700 da raunata mutum 63,740. 1123 GMT — An yi wa mutum 20 kisan kiyashi a mahadar kasar Kuwait a Gaza — Ma...
