Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Kai-tsaye: Isra'ila ta yi luguden wuta a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke Gaza

Yaƙin kisan ƙare-dangi da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana 431 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,758 tare da jikkata mutum fiye da 106,134. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum fiye da 4,047 tun daga Oktoban 2023. Talata, 10 ga watan Disamba, 2024 0705 GMT — Dakarun Isra'ila sun kashe...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta yi luguden wuta a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke Gaza
Kwa muhtasari

Yaƙin kisan ƙare-dangi da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana 431 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,758 tare da jikkata mutum fiye da 106,134. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum fiye da 4,047 tun daga Oktoban 2023. Talata, 10 ga watan Disamba, 2024 0705 GMT — Dakarun Isra'ila sun kashe...

Yaƙin kisan ƙare-dangi da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana 431 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,758 tare da jikkata mutum fiye da 106,134. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum fiye da 4,047 tun daga Oktoban 2023. Talata, 10 ga watan Disamba, 2024 0705 GMT — Dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa bakwai, ciki har da wata mata da 'ya'yanta uku tare da jikkata gommai a hari ta sama da suka kai da sanyin safiya a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza. A wata sanarwa da ta fitar, rundunar kare fararen-hula ta yankin ta ce tawagarta ta gano gawawwakin mutanen bakwai a gidan iyalan "Khalifa" da ke sansanin na Nuseirat. Wata majiya daga asibitin al-Awda ta ce an kai mutanen, ciki har da wata mata da 'ya'yanta, asbitin tare da waɗanda suka jikkata. Kazalika harin na Isra'ila ya rusa gidan tare da lalata gidajen da ke maƙotaka, a cewar wasu ganau da suka yi hira da kamfanin labarai na Anadolu . Ƙarin bayani ???? 2300 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 25 a arewacin Gaza Sojojin Isra'ila sun kashe iyalan Falasɗinawa biyu bayan sun yi luguden wuta a gidansu a garin Beit Hanoon da ke arewacin Gaza. "Sojojin Isra'ila sun yi luguden wuta a wani gida da iyalai biyu 'yan ƙabilar Al-Kahlout, inda mutum 25 suke zaune, inda ginin ya rufta akansu," a cewar ɗaya daga cikin 'yan'uwansy mai suna Abdel Rahman Al-Kahlout. "Isra'ila ta sake gudanar da kisan kiyashi, inda ta kashe iyalai biyu gaba ɗaya," in ji shi. Ya ƙara da cewa har yanzu gawarwakin suna ƙarƙashin ɓaraguzai saboda hatsarin da ke tattare da zuwa ɗebo su.