Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Kai-tsaye: Isra'ila ta umarci sojojinta su ƙara ƙaimi wurin kai hare-hare a Gaza

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 318, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,099 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 92,609, kana an ƙiyasta cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka rusa. Litinin, 19 ga watan Agusta, 2024 2213 GMT — I...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta umarci sojojinta su ƙara ƙaimi wurin kai hare-hare a Gaza
Em resumo

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 318, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,099 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 92,609, kana an ƙiyasta cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka rusa. Litinin, 19 ga watan Agusta, 2024 2213 GMT — I...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 318, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,099 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 92,609, kana an ƙiyasta cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka rusa. Litinin, 19 ga watan Agusta, 2024 2213 GMT — Isra'ila ta yanke shawarar ci gaba da luguden wuta a yankin Gaza da ta mamaye domin ƙara samun dama a shirin tattaunawa ta tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni, in ji wata jaridar Isra'ila da ake wallafawa a shafin intanet. "Kwanakin baya majalisar tsaron Isra'ila ta bayar da umarni ga sojoji su ƙara ƙaimi a hare-haren da suke kai wa Gaza da zummar ƙarfafa matsayinsu a wajen tattaunawar da ake yi," in ji jaridar Walla, wadda ta ambato wasu majiyoyi na siyasa. 2314 GMT — Biden ya ce har yanzu yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza 'mai yiwuwa ce' Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya yi amanna har yanzu yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza "mai yiwuwa ce". Har yanzu "ana ci gaba da tattaunawa. Ba za mu karaya ba. Abu ne mai yiwuwa," kamar yadda Biden ya shaida wa manema labarai. 2237 GMT — Sojojin Isra'ila sun jikkata wata Bafalasɗiniya 'yar jarida da ke aika rahotanni daga Gaza Sojojin Isra'ila sun jikkata wata Bafalasɗiniya 'yar jarida da ke aika rahotanni daga yankin Khan Younis na Gaza da aka mamaye. Dakarun mamaya na Isra'ila sun yi harbi kai-tsaye kan wata tawagar 'yan jarida, inda suka samu Salma al-Qadoumi a baya, kamar yadda ganau suka shaida wa Anadolu Agency.