Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwanaki 316 yanzu, ya kashe fiye da Falasdinawa 40,00 akasari mata da ƙananan yara tare da jikkata mutum fiye da 92,400, an ƙiyasta fiye da 10,000 na binne a ƙarƙashin baraguzan gine-ginen da aka kai musu hari. Asabar, 17 ga August, 2024 0835 GMT — Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Asabar ta sake bayar da sabuwar sanarwar hijira inda ta umarci mazauna wasu unguwanni a tsakiyar Gaza su yi hijira. Mai magana da yawun sojin Avichay Adraee ne ya sanar da hakan inda ya ce mazauna rukunin gidaje na 2232 zuwa 2240 da ke unguwar Maghazi da kuma waɗanda ke unguwannin Salah El-Din, El-Farouk da kuma El-Amal duk a tsakiyar Gaza su yi hijira daga wuraren. Sojojin sun yi iƙirarin cewa wuraren na cikin mummunan hatsari sakamakon yaƙin da ake yi da Hamas. 0016 GMT — Isra'ila ta kashe aƙalla mutane shida ta kuma jikkata mutum uku a wani hari da ta kai rukunin gidajen zama a birnin Nabatieh, a kudancin Labanan, a cewar Ma'aikatar Lafiyar Labanan. Hankula sun tashi a yankin a ’yan makonnin nan, bayan Isra'ila ta yi wa wani babban kwamandan Hezbollah kisan gilla a wajen birnin Beirut. Hezbollah ta kuma sha alwashin ɗaukar fansa a kan Isra'ila saboda kisan da ta yi wa shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa Ismail Haniyeh a Tehran. 0030 GMT — Biden yana da 'kyakkyawan fata' a kan tattaunawar zaman lafiya a Gaza Shugaban Amurka Joe Biden ya ce yana da 'kyakkywan fata' dangane da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. "Har zuwa awa ɗaya da ta wuce, har yanzu ana kan tattaunawa, ina da kyakkyawan fata. An kusa cim ma matsaya. Wasu 'yan batutuwa ne kawai suka rage. Ina ji mun yi dace," kamar yadda Biden ya shida wa manema labarai lokacin da aka tambaye shi dangane da tattaunawar. "Abu ne da za a sa ido a gani," a cewar Biden lokacin da aka tambaye shi ko zuwa yaushe za a fara tsagaita wutar. Biden ya ce kada wani a Gabas ta Tsakiya "ya ɗauki wani mataki da zai kawo cikas ga shirin."
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
Kai-tsaye: Isra'ila ta umarci mazauna wasu yankuna a Gaza su yi hijira
Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwanaki 316 yanzu, ya kashe fiye da Falasdinawa 40,00 akasari mata da ƙananan yara tare da jikkata mutum fiye da 92,400, an ƙiyasta fiye da 10,000 na binne a ƙarƙashin baraguzan gine-ginen da aka kai musu hari. Asabar, 17 ga August, 2024 0835 GMT — Rundunar...

Кратко
Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwanaki 316 yanzu, ya kashe fiye da Falasdinawa 40,00 akasari mata da ƙananan yara tare da jikkata mutum fiye da 92,400, an ƙiyasta fiye da 10,000 na binne a ƙarƙashin baraguzan gine-ginen da aka kai musu hari. Asabar, 17 ga August, 2024 0835 GMT — Rundunar...
