الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta umarci Falasɗinawa 88,000 su fice daga yammacin Gaza

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 117 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 26,751 sannan suka jikkata mutum 65,636, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 0830 GMT — Isra'ila ta umarci Falasɗinawa 88,000 su fice daga yammacin Gaza Isra'...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
KAI-TSAYE: Isra'ila ta umarci Falasɗinawa 88,000 su fice daga yammacin Gaza
لمحة سريعة

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 117 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 26,751 sannan suka jikkata mutum 65,636, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 0830 GMT — Isra'ila ta umarci Falasɗinawa 88,000 su fice daga yammacin Gaza Isra'...

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 117 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 26,751 sannan suka jikkata mutum 65,636, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 0830 GMT — Isra'ila ta umarci Falasɗinawa 88,000 su fice daga yammacin Gaza Isra'ila ta ƙara bayar da wani sabon umarni ga Falasɗinawa akalla 88,000 waɗanda suka rasa muhallansu da ke zaune a yammacin birnin Gaza kan su tashi daga wurin, kamar yadda Hukumar Kula da Ayyukan Jin Kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar. Yankin wanda ya haɗa da sansanin ƴan gudun hijira na Ash Shati, ya kasance wuri da ke da mazauna kusan 300,000 kafin fara yakin. Tun bayan fara wannan yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba Isra'ila ta bai wa mazauna Gaza wa'adi kan su fice daga birnin.